Idan ka dubi tutocin ƙasashen Afirka da kyau suna da wani salon kamanni da junansu. Yawancin tutoci 54 na ƙasashen suna da aƙalla kala ɗaya cikin waɗannan kalolin, wato kore, yalo, ko ja.
Wannan ba arashi ba ne. Yana da tushe a tarihi, siyasa, da fafutukar neman 'yancin-kai.
Baiɗaya ana kiran waɗannan rukunin kaloli da kalolin kishin Afirka, kuma mafi muhimmancin madogarar asalinsu shi ne Habasha.
Ƙasar tana da muhimmin gurbi a tarihin Afirka kasancewar ita ce ƙasa ɗaya tilo da ta yi nasarar bijirewa mulkin mallaka daga Turawa, inda ta yi galaba kan Italiya a Yaƙin Adwa a 1896.
Bayan wannan muhimmiyar nasara, Habasha ta zaɓi kalolin tutarta, wato kore, yalo, da ja, waɗanda suka zamo ƙaƙƙarfar alama ta 'yancin Afirka a lokacin da yawancin nahiyar ke ƙarƙashin mulkin mallaka.
Yayin da ƙungiyoyin gwagwarmayar neman 'yanci suka samu ƙarfi a shekarun 1950 da 1960, sabbin ƙasashen Afirka ba su tsara tutarsu a kaɗaice ba.
Manufofin masu alƙa
Da yawan ƙasashe na nuna cewa suna da alaƙa da junansu a manufofi, gadon tarihi, da kuɓuta daga mulkin mallaka a tare.
A shekarar 1957, Ghana ta zama ƙasar Afirka ta farko a kudu da Sahara wada ta samu ’yancin-kai. Shugabanninta sun karɓi tsarin launukan kishin Afirka kuma sun ƙara tauraro baƙi, inda suka mayar da tutar tamkar bayyanannen jawabin haɗin-kan Afirka da mulkin-kai.
Masharhanta na ganin cewa ƙarfin Ghana a yankin da ma a duniya ya taimaka wajen bazuwar wannan salon gani a faɗin nahiyar.
Sauran ƙasashe sun daidaita launukan zuwa yanayinsu, kodayake tare da ɗan bambanci a ma'ana da kamanni; inda tawagogin ƙwallo na ƙasashen suke ɗaukar irin waɗannan launuka da zane a rigunansu.
Guinea ta ɗauki launukan uku a tsaye; Mali ta yi amfani da irin tsarin haka amma da wani jere launin daban, yayin da Kamaru da Senegal suka ƙara taurari don ƙarfafa haɗin-kai, alamar ƙasa, da walƙiya.
Jamhuriyar Kongo ta shimfiɗa waɗannan launuka a layin kusurwa, tana haɗa su da albarkatun daji, abota, da gwagwarmayar neman ’yanci.
Benin da São Tomé da Príncipe ma sun yi amfani da wannan zubi yayin da suke jaddada tarihin gida da yanayin ƙasa.
Ko da cewa launukan sun yaɗu, ana fayyace ma'anarsu a matakin ƙasa. Gabaɗaya, ja yana wakiltar jinin da aka zuba a gwagwarmayar yaƙi da mulkin mallaka, rawaya na nuna arziƙin ma'adinai da hasken rana, yayin da kore ke alamta aikin gona, wadata, dazuka, da sauran albarkatun halitta.












