| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Kenya ta ƙaddamar da kyamarorin ɗaurawa a jikin jami’an kwastam don yaƙi da rashawa
Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Kenya ta ce kyamarorin na da karfin ikon tsawatarwa game da cin hanci da rashawa kuma bidiyon da za a dauka zai hanzarta warware rikici.
Kenya ta ƙaddamar da kyamarorin ɗaurawa a jikin jami’an kwastam don yaƙi da rashawa
Ma'aikata daure da kyamara a jikinsu a babban filin jiragen sama na Kenya. PHOTO / KRA / Others
10 Maris 2026

Hukumar tara kudaden shigar ta ce Kenya ta fitar da kyamarorin da ake sanya wa jiki ga jami'an kwastam da na kula da kan iyakoki don taimakawa wajen sauƙaƙe ciniki da tafiye-tafiye na halal.

Wannan matakin zai sa a sanya kyamarorin jiki guda 350 a cibiyoyin kan iyakoki kuma an yi hakan ne don "sauƙaƙa ciniki da tafiye-tafiye na halal".

Kenya ita ce babbar cibiyar tattalin arzikin Gabashin Afirka kuma tana gudanar da Filin Jirgin Sama na Jomo Kenyatta (JKIA) - ɗaya daga cikin cibiyoyin sufuri mafi cunkoso a Afirka.

Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Kenya ta ce kyamarorin suna da ƙarfi wajen hana cin hanci da rashawa kuma hotuna da bidiyo za su tabbatar da warware takaddama cikin sauri.

"Lokacin da kyamarar ke juyawa, nuna ƙwarewa ba zaɓi ba ne; shi ne aikinta na asali. Mu’ama;lar da aka dauka a bidiyo da hoto na martaba kowa,” jn jinhukumar a ranar Talata.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da ake damuwa game da cin hanci da rashawa na ma'aikata da shirye-shiryen haɗin gwiwa na waɗanda ke kaucewa biyan haraji ga kasa?.

"Mun himmatu ga yin adalci. Mun himmatu ga aminci. Kuma muna son a ɗora mana alhakin hakan," in ji mai karɓar haraji.

Rahotannin cikin gida sun nuna cewa na'urorin suna da fasahar bin diddigi ta GPS kuma nuna komai kai tsaye, suna da karfin nadr bayanai, tsaro kuma suna iya watsa shirye-shirye kai tsaye.

Rumbun Labarai
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasar Djibouti Guelleh ya sake yin nasara karo na shida
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Djibouti inda Guelleh da ke mulki ke neman wa'adi na shida
Daga hanyoyin mulkin mallaka zuwa na korar mutane: Afirka da siyasar korar baƙi daga wata ƙasa
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Shugaban riƙon jihar Kudu maso yammacin Somaliya zai hau kan mulki bayan ajiye aikin shugaba
Sudan ta nemi 'yan ƙasar da suka yi ƙaura zuwa ƙasashen waje saboda yaƙi su koma gida