Ɗumbin magoya bayan Kwankwasiyya sun halarci taron komawar Kwankwaso Jam'iyyar ADC

Tsohon Ministan Tsaron na Nijeriya ya yi rajista da jam’iyyar ADC kuma ya karɓi katin shaidar zama ɗan jam’iyya a Gidan Kwankwasiyya da ke kan titin Miller Road, Bompai, Kano.

By
Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023, inda ya zo na huɗu. / Rabi'u Musa Kwankwaso Facebook

Shugabannin jam’iyyar ADC da ɗumbin magoya baya, musamman daga Ƙungiyar Kwankwasiyya, sun halarci taron sauya sheƙar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso inda ya koma Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance.

Tsohon Ministan Tsaron na Nijeriya ya yi rajista da jam’iyyar ADC kuma ya karɓi katin shaidar zama ɗan jam’iyya a Gidan Kwankwasiyya da ke kan titin Miller Road, Bompai, Kano.

Ya kuma sanar da sauya sheƙarsa a shafinsa na X.

 “Sabuwar Asubahi. Mu ne ADC,” in ji tsohon gwamnan a ranar Litinin.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark; Sakataren jam’iyyar na ƙasa kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola; da kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Sanata Dino Melaye; tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Cif John Odigie-Oyegun; da kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamna Peter Obi, waɗanda manyan abokan hamayyar Tinubu ne sun zama fuskar Jam’iyyar ADC.

Kwankwaso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023, inda ya zo na huɗu. Abubakar da Obi sun zo na biyu da na uku bi da bi.

A ranar Lahadi, Kwankwaso ya sanar da cewa ba kawai zai sauka daga shugabancin NNPP ba, har ma zai fice daga jam’iyyar gaba ɗaya, yana mai cewa “halin da siyasar ƙasar ke ciki a yanzu” na buƙatar “sake tsara tafiya bisa dabara.”

Wannan sauyi ya zo ne ƙasa da shekara guda kafin babban zaɓen Nijeriya na gaba. Jam’iyya mai mulki ta amince da Shugaba Tinubu ya nemi wa’adi na biyu a zaɓen Janairu na 2027, kuma ana sa ran zai tsaya takara.