Me zai faru idan uwa, wadda ake sa ran ita ce ginshiƙin tarbiyyar iyali, ta
tsinci kanta cikin ta'ammali ko dillancin miyagun ƙwayoyi? A Nijeriya, musamman arewacin ƙasar, wannan tambayar ba zato ba ce.
Matsala ce da hukumomi ke cewa tana ƙara bayyana a zahiri.
An daɗe ana kallon maza musamman matasa a matsayin waɗanda suka fi
faɗawa cikin halayyar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Amma yanzu, wata
sabuwar barazana na ƙara bayyana a wasu jihohi kamar Jihar Kano.
Mata ciki har da matan aure, da mata masu shekarun suna ƙara shiga
ta’ammuli da kwayoyi. Kuma masana na gargadin cewa idan uwa ta lalace,
iyali da al'umma baki ɗaya na iya fuskantar mummunan sakamako.
Sabbin alkaluman Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta
Nijeriya (NDLEA) reshen jihar Kano sun nuna cewa daga watan Janairu
zuwa Yuli na shekarar 2026, hukumar ta kama mutane 904 da ake zargi da
hannu a harkar miyagun ƙwayoyi, ciki har da mata 35.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya shaida
wa TRT Afrika Hausa cewa duk da cewa adadin matan bai kai na maza ba,
abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke
amfani da mata, musamman matan aure, wajen adanawa da dillancin
ƙwayoyi a cikin unguwanni.
A cewarsa, masu wannan haramtacciyar sana'a na shiga gidajen aure ta
hanyar yaudarar mata da kuɗi ko wasu alfanun rayuwa, inda wasu daga
cikinsu ke shiga harkar ba tare da mazajensu sun sani ba.
NDLEA ta ce Kano na cikin jihohin da matsalar ta fi kamari, inda ake kiyasta
cewa kusan mutane miliyan biyu na amfani da wasu nau'ukan miyagun
ƙwayoyi a jihar mai yawan al’umma kusan miliyan 20.
Sai dai tambayar ita ce: me ya sa mata ke rungumar wannan mummunar
rayuwa? Kuma me hakan ke nufi ga makomar al'umma?
Masana na bayyana cewa idan mace ta faɗa cikin ta'ammali ko safarar
miyagun ƙwayoyi, illar ba ta tsaya kanta kaɗai ba. Mace ita ce ginshiƙin iyali
kuma mafi tasiri kan tarbiyyar yara, da gina ɗabi'u da zaman lafiyar gida.
Idan ta faɗa cikin wannan mummunar dabi'a, haɗarin ya kan shafi lafiya da
tarbiyyar yara, zaman lafiyar iyali, da kuma al'umma baki ɗaya.
Hakan na iya janyo a wayi gari da yara da za su taso cikin rashin kulawa,
tashin hankali, ko ma tsunduma cikin irin wannan matsala.
Wani bincike da masana suka gudanar a ƙaramar hukumar Dala a jihar ta
Kano a shekarar 2025 ya nuna cewa kusan kashi 42 cikin 100 na matan da
aka yi bincike a kansu sun taɓa amfani da ƙwayoyi masu sa maye,
musamman magungunan tari masu ɗauke da codeine, da tramadol da wiwi.
Binciken ya danganta wannan matsala da talauci, rashin aikin yi, matsin
rayuwar aure, da kuma ƙarancin ilimi.
Haka kuma, wani binciken National Drug Use Survey da gwamnatin Nijeriya
da Hukumar Yaƙi da Safara da Ta'ammali da Ƙwayoyi ta Majalisar Ɗinkin
Duniya (UNODC) suka gudanar a shekarar 2018, ya nuna cewa mata na
cikin manyan masu amfani da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya, a cikin kimanin
mutane miliyan 14.3 da aka kiyasta suna ta'ammali da ƙwayoyi a ƙasar mai
al’umma kusan miliyan 230.
A lokuta da dama, an ambato Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yana kira
ga iyaye, shugabannin al'umma da hukumomi da su haɗa kai wajen yaƙi da
matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Ya jaddada cewa yawaitar ta'ammali da ƙwayoyi tsakanin matasa da mata na iya jefa makomar al'umma cikin babban haɗari.
A cewar NDLEA, baya ga kama masu laifi da lalata hanyoyin safarar
miyagun ƙwayoyi, hukumar na ƙara mayar da hankali kan wayar da kai da
ilimantar da al'umma, musamman mata da matasa, domin hana su fadawa
tarkon wannan mummunar jaraba.
Yayin da matsalar ke ƙara yaduwa, masana na gargadin cewa magance ta
ba aikin gwamnati kaɗai ba ne.
Suna cewa dole ne iyaye, malamai, shugabannin addini da al'umma bakiɗaya su haɗa hannu wajen kare mata da matasa daga fadawa cikin ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi, domin kare iyali da makomar al'umma.


















