Fiye da gidaje 1,000 a Tel Aviv sun lalace sun zama kufai sakamakon hare-haren baya bayan nan na Iran a yakin da Isra’ila da Amurka ke yi da ita, kamar yadda magajin garin birnin ya bayyana a ranar Asabar.
Tashar Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito Ron Huldai na cewa “ba a za a iya sake zama a cikin fiye da gidaje 1,000 a Tel Aviv ba” sakamakon barnar da makaman roka da jirage marasa matuƙa na Iran suka yi.
A lokacin yaƙin da Amurka da Isra’ila suka yi da Iran, wanda ya fara a ranar 28 ga Fabrairu, Tehran ta rika kai hare-hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan manyan biranen Isra’ila a matsayin martani ga hare-haren da aka kai mata.
Wasu daga cikin makaman da kuma tarkacen da suka samo asali daga yunƙurin kakkabo su sun fāɗa kan gine-gine a Tel Aviv, Ramat Gan da Bnei Brak, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da raunata mutane da dama, tare da jawo babbar barna ga gidaje, motoci da kayayyakin more rayuwa.
Channel 12 ta kuma ruwaito a farkon wannan mako cewa jami’an Isra’ila na kiyasta kuɗin da aka kashe cikin kwanaki 40 na yaƙi da Iran da Lebanon ya kai kimanin dala biliyan 17.5.
Adadin da aka bayyana bai haɗa da kuɗin sake gina gine-gine ko asarar da aka yi sakamakon raguwar ayyukan tattalin arzikin Isra’ila yayin yaƙin ba.
A cewar kafafen yaɗa labarai na Isra’ila, kusan mutum 30,000 sun gabatar da ƙorafe-ƙorafe ga Asusun Diyya na Hukumar Haraji ta Isra’ila kan asarar dukiya kai-tsaye, ciki har da ƙorafe-ƙorafe 18,408 da suka shafi gine-gine, 2,594 kan kayayyaki, da kuma 6,617 kan motoci.
Shafin tattalin arziki na Isra’ila, Calcalist ya ruwaito a makon da ya gabata cewa yaƙin kwanaki 12 da aka yi da Iran a watan Yunin bara ya jawo biyan diyya kusan shekel biliyan 3 (dala biliyan 1) ga ‘yankasuwa.
Ma’aikatar Kuɗi ta Isra’ila kuma na kiyasta cewa kuɗin diyya na yaƙin da aka yi tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 8 ga Afrilu zai kai shekel biliyan 6.5.
Tattaunawar tsagaita wuta da aka gudanar a babban birnin Pakistan a ranar 8 ga Afrilu bayan tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, ya gaza kai ga cim ma yarjejeniya ta ƙarshe don kawo ƙarshen yaƙin.










