Fatan ganin haske: Dalilan da suka sanya har yanzu ‘yan Afirka miliyan 560 ke jiran samun lantarki
AFIRKA
8 minti karatu
Fatan ganin haske: Dalilan da suka sanya har yanzu ‘yan Afirka miliyan 560 ke jiran samun lantarkiWani rahoton 2026 kan cigaban makamashi ya bayyana cewa har a yankunan da ke da hanyoyin raba lantarki, kudin jona wutar, kudaden hada wayoyi a yankunan, da cigaban tsadar lantarkin sun zama kalubalen da aka gaza magancewa ga gidajen marasa galihu.
Kimanin mutane miliyan 560 ne ke rayuwa ba tare da wutar lantarki ba a fadin Afirka - har ma a inda ake da kayan bayar da wutar. Photo: Others

Rana tana haskakawa a kan busasshiyar ƙasa ta gundumar Turkana da ke arewa maso-yammacin Kenya, inda yanayin zafi ke ƙaruwa sama da digiri 40 a ma’aunin Celsius.

A nan, a ɗaya daga cikin yankunan da ke da nisa kuma ke fama da talauci a ƙasar, Akiru Lokwang ta shafe tsawon rayuwarta tana kallon tashar rarraba wutar lantarki ta ƙasa tana wucewa kamar alƙawarin da ba ya zuwa.

Akiru mai shekaru arba'in da uku, uwa ce mai 'ya'ya biyar kuma kaka ga 'ya'ya biyu, tana zaune a wani ƙaramin gida a wajen Lodwar.

Daga gidanta, tana iya ganin layukan rarraba lantarki da aka shimfiɗa a kan turaku —na ƙarfe da ke ɗauke da wutar lantarki daga masana'antun ‘Rift Valley’ zuwa sauran sassan ƙasar. Layin rarraba wutar lantarki yana nana a nisan 'yan kilomita daga gidanta. Duk da haka ba a taɓa haɗa wutar ba.

"Ina ganin turakun a kowace rana," Akiru ta shaida wa TRT Afirka, muryarta tana ɗauke da mika wuya da kuma kin amincewa.

"Suna tsaye a wurin kamar shaidu da ba sa magana game da gwagwarmayarmu. Wutar lantarki tana ratsa wa ta saman kawunanmu, amma wataƙila tana can a duniyar wata.

Gwamnati ta ce layin wutar lantarkin yana nan, amma menene amfanin idan ba za mu iya amfani da shi ba? Kudin haɗa wutar ya fi abin da nake samu a watanni uku.”

Yanayin Akiru ya nuna mummunan rikici wanda ke bayyana talaucin makamashi a faɗin Afirka: akwai kayan more rayuwa, amma arha na sa miliyoyin mutane su shiga cikin mawuyacin hali.

‘Makamashi rayuwa ne’

Sabon Rahoto na Bibiyar Manufar Ci Gaba Mai Dorewa ta 7 (SDG 7): Rahoton Cigaban Makamashi, wanda aka fitar a watan Yulin 2026, ya nuna cewa har a yankunan da ke da hanyoyin raba lantarki, kudin jona wutar, kudaden hada wayoyi a yankunan, da cigaban tsadar lantarkin sun zama kalubalen da aka gaza magancewa ga gidajen marasa galihu.

A faɗin yankin kudu da hamadar Sahara, mutane miliyan 560 suna rayuwa ba tare da wutar lantarki ba - adadi mai ban mamaki wanda ya haura dukkan al'ummar Tarayyar Turai.

Bugu da ƙari, akwai 'yan Afirka miliyan 970 waɗanda ba su da damar samun mafita mai tsabta a bangaren girki, kuma a yanzu kun fara fahimtar girman rikicin.

Kilomita dubu biyar daga yamma, a Legas, Najeriya, Adebayo Ogunlesi yana gudanar da ƙaramin shagon dinki a unguwar Ajegunle mai cike da jama'a.

Ya zuba jarin dala 800 a injin dinki da ƙaramin janareta bayan layin wutar lantarki na ƙasa na Najeriya ya ba shi kunya sau da yawa. Amma farashin man fetur na janareta na cinye rabin ribar da yake samu.

"Mutane suna magana game da makomar makamashi kamar dai abin jin daɗi ne," in ji Adebayo, hannunsa a kwance saboda shekaru da ya yi yana yankan yadi da hannu.

"Amma a wajen mu, makamashi shi ne rayuwa. Shagona yana buƙatar wutar lantarki don gudanar da aiki. 'Ya'yana suna buƙatar wutar lantarki don yin karatu. Matata tana buƙatar girki mai tsafta don kiyaye lafiyar iyalinmu.

Kowace rana, ina ƙona kuɗi akan man fetur don kunna janareta, kuma kowace rana, ina kallon hayakin wutar girki yana cika gidanmu. Muna biyan kuɗi sau uku - a cikin kuɗi, a cikin lafiya, da kuma a cikin ɓatacciyar dama."

Bacin ran Adebayo ya fito da babban sakamakon binciken: damar saye ta kasance babban cikas ga faɗaɗa damar wutar lantarki.

Yanayin samar da wutar lantarki a yankin kudu da hamadar Sahara ya ragu sosai, kuma rahoton ya yi gargaɗin cewa ci gaba dole ne ya ninka sau uku don cim ma burin samun damarmaki na duniya nan da 2030.

Makamashi daga hasken rana

Duk da haka, a tsakanin alkaluman da ba su da kyau, akwai kyakkyawan fata. Rahoton ya nuna cewa makamashi mai sabuntuwa a yanzu yana samar da sama da kashi 30 cikin 100 na amfani da wutar lantarki a duniya, kuma karfin samar da makamashin da ake sabuntawa ya kai matsayin watt 544 ga kowane mutum a duniya.

Mafitar makamashi mai sabuntuwa da aka rarraba - gami da na'urorin hasken rana da ƙananan na'urori - sun riga sun yi wa ɗaruruwan miliyoyin mutane hidima, suna ba da hanya mai arha ga samar da wutar lantarki ga al'ummomi masu nisa.

"Kungiyar IEA tana aiki tare da gwamnatoci, masana'antu da abokan hulɗa na ƙasashen duniya don hanzarta saka hannun jari da dukar matakan dabbaka manufofi da ake buƙata don cim ma damar shiga duniya baki ɗaya, musamman don dafa abinci mai tsafta," in ji Fatih Birol, Babban Darakta na Hukumar Makamashi ta Duniya.

"Duk da cewa SDG7 manufa ce ta makamashi, fa'idojinsa sun wuce fannin makamashi - sun hada da inganta lafiya, faɗaɗa damar tattalin arziki, ƙarfafa tsaro da gina al'ummomi masu juriya."

Amma girman jarin da ake buƙata ya kasance mai ban tsoro. Gudunmawar kuɗi na jama'a na ƙasashen duniya waɗanda ke tallafawa makamashi mai tsafta a ƙasashe masu tasowa ya ƙaru kaɗan zuwa dala biliyan 24.6 a shekarar 2024 - adadi ne mai yawa amma kuma bai isa ba idan aka yi la'akari da girman ƙalubalen.

Ga ƙasashen da ba su da ci gaba sosai, waɗannan cigaba sun ragu da kashi 11 cikin ɗari, inda suka yi samu daukar bayanan dala biliyan 3.7 kacal.

Kuɗin da aka samu ta hanyar bashi ya ci gaba da mamaye yankin, wanda ya kai kashi 80 cikin ɗari na jimillar kudaden da suka shigo.

"Girman makamashi na baya-bayan nan a duniya ya bayyana abu ɗaya a sarari: ƙasashen da ke da ƙarfin makamashi mai sabuntawa sun fi dacewa su jure wa katsalandan din tattalin arziki da jigilar kayayyaki," in ji Francesco La Camera, Darakta Janar na Hukumar Makamashi Mai Sabuntawa ta Duniya.

"Dole ne haɓaka aika makamashi mai sabuntawa na cikin gida mai kyakkyawan farashi ya zama muhimmin abu don ƙarfafa tsaron makamashi da juriyar tattalin arziki, yayin da ake bin ka’idojin SDG 7.

Don cim ma wannan, dole ne al'ummar duniya su ba da fifiko ga tallafin kuɗi mai sauki da aka tsara, musamman ga ƙasashen da ba su da ci gaba."

Ba za a iya yin watsi da sakamakon lafiya da rashin aukar matakan da suka dace ke janyo wa ba. Gurɓatacciyar iskar gida daga man girki ce ke haifar da mutuwar kusan mutane miliyan 3 a kowace shekara - boyayyen bala'i da ke shafar mata da yara da yawa.

Manufofin Lafiya

Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana kalubalen da kyau: "Samun makamashi mai tsafta da dorewa a duniya ba wai kawai kalubalen makamashi ba ne; muhimmin abu ne na lafiya. Gurɓatar iskar gida daga man girki yana kashe miliyoyin rayuka, yana haifar da cututtuka da nakasa na dogon lokaci, kuma yana cutar da muhallinmu."

A yankin kudu da hamadar Sahara, gibin wutar lantarki a yankunan karkara ya karu daga miliyan 376 a shekarar 2010 zuwa miliyan 447 a shekarar 2024. Ba tare da daukar matakin gaggawa ba, ana sa ran adadin mutanen da ba su da damar yin girki mai tsafta a yankin zai kai biliyan daya nan da shekarar 2027.

Bambancin da ke tsakanin karkara da birane yana ƙara ta'azzara rikicin. Yayin da kashi 89 cikin 100 na al'ummar birane ke da damar yin girki mai tsafta, kashi 56 cikin 100 na mazauna karkara ne kawai ke da wannan damar.

Yayin da shugabannin duniya suka taru a babban taron siyasa kan ci gaba mai dorewa a New York daga 7 zuwa 15 ga Yuli 2026, sakon ya bayyana karara: saurin ci gaban da ake samu a yanzu bai wadatar ba.

Samun wutar lantarki a duniya ya tsaya cak a kashi 92 cikin 100, kuma ci gaban shekara-shekara ya ragu da rabi idan aka kwatanta da shekaru goma da suka gabata.

"Matsalar makamashi a duniya a yanzu tana ba da dama don hanzarta sauyawa zuwa makamashi mai tsafta don tallafawa tsaron makamashi," in ji Li Junhua, Mataimakin Sakatare Janar na Tattalin Arziki da Harkokin Jama'a a Majalisar Dinkin Duniya.

"Amfani da wannan damar zai buƙaci ƙarin tallafi da saka hannun jari daga ƙasashen waje. Ba za mu iya biyan buƙatunmu ba. Lokaci ya yi da za mu yi aiki cikin gaggawa da neman cika buri."

A wajen Akiru Lokwang da ke Turkana da Adebayo Ogunlesi da ke Legas, ƙididdigar ba su da wani tasiri - su ne yanayin rayuwar yau da kullum. Kowane maraice ba tare da wutar lantarki ba dama ce da aka rasa. Kowane abinci da aka dafa a kan gawayi hatsari ne ga lafiya.

Yayin da rana ke faɗuwa a saman shimfidaddiyar kasa ta Turkana, Akiru ta tattara jikokinta a kusa da ƙaramar fitilar kananzir, harshenn wutar fitilar mai walƙiya na jefa dogayen inuwa a bangon dakunansu.

Ta cikin ƙofar dakin, za ta iya ganin layukan rarraba lantarki da aka girke - abin tunawa koyaushe game da ikon da ke ratsa gidanta amma ba ta samun sa.

"Ka san me ke sa ni ci gaba?" ta faɗi a hankali, muryarta tana ɗauke da juriya da hamada mai tsauri ta ƙirƙira tsawon shekaru da yawa.

"Imani da cewa jikokina ba za su rayu haka ba. Wata rana, idan suka kunna fitila, za ta ci gaba da aiki.

“Za su dafa abinci ba tare da hayaki ya kona musu ido ba. Samun wutar lantarki bai kamata ya dogara da adadin kuɗin da ke aljihunka ba."