Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce babu wani batun tattaunawa a yanzu haka da Amurka, kwanaki uku bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamarwa da kasarsa da hare-hare ta sama.
Ali Bahreini, jakadan Iran a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa Iran ba ta tuntubi Amurka kai-tsaye ko ta hannun wani ba game da a tattauna da manufar kwantar da hankula ko kuma wai a dawo teburin tattaunawa kan shirin Nukiliya na Tehran.
Da aka tambaye shi kan yiwuwar wata tattaunawa sai ya ce: “A yanzu dai muna tantama sosai game da amfanin tattaunawa… yare guda daya da Amurka ke fahimta shi ne na kare kai.”
Ya kara da cewa “Ba na tunanin yanzu lokaci ne na yin wata tattaunawa daga bangarenmu.”
A ranar Alhamis din da ta gabata wakilan Iran da Amurka suka zauna a Geneva, inda mai shiga tsakani Oman ta bayyana cewa an samu cigaba, amma kwanaki biyu bayan hakan Amurka da Isra’ila suka fara kai wa Iran hare-haren hadin gwiwa ta sama, har ma suka kashe Jagoran Addininta Ali Khamenei da wasu manyan jami’an Iran wanda hakan ya janyo rikici a yankin.
Budaddun amsoshi
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan kasashen Gulf makota da kuma Isra’ila sannan ta kuma rufe hanyar mashigar teku ta Hormuz inda ake fitar da kashi daya cikin biyar na albarkatun mai da iskar gas da duniya ke bukata.
A ranar Talata an sake samun fashewar abubuwa a Tehran, kuma kasuwanin duniya sun rikice a yayin da ake tsoron rikicin na iya tsawaita da kawo cikas ga jigilar makamashi a duniya. Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun bayar da amsoshi budaddu a lokacin da ak tambaye su yaushe ne za a daina yakin.
Trump ya ce yana ganin yakin zai dauki tsawon makonni biyar, inda Netanyahu kuma ya ce ‘ba zai dauki tsawon shekaru ba”.
Wata majiya da ke da kusanci da shirin yaki na Isra’ila a ranar Talata ta ce gangamin Isra’ila shi ne na makonni biyu kuma yana yin sauri sama da yadda ake tsammani.













