Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinci
NIJERIYA
3 minti karatu
Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinciA cikin watan Yunin da ya gabata kaɗai, rahotanni sun bayyana cewa an kashe manoma fiye da 100 a hare-hare daban-daban da aka kai a jihohi da dama.
Hare-hare na zuwa ne a muhimmin lokaci na damina, abin da ke ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar raguwar amfanin gona, da tashin farashin abinci. / Reuters

Rashin tsaro a arewacin Nijeriya na ƙara ƙamari inda a cikin ‘yan kwanakin nan ‘yan ta’adda a jihohi daban-daban na arewacin ƙasar suka rinƙa bin manoma har gonakinsu suna kashe su, lamarin da ke ƙara bayyana irin matsalar rashin tsaro da ke addabar yankunan karkara da kuma tasirin matsalar ga samar da abinci.

A cikin watan Yunin da ya gabata kaɗai, rahotanni sun bayyana cewa an kashe manoma fiye da 100 a hare-hare daban-daban da aka kai a jihohi da dama.

A Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, an kashe manoma 17, yayin da wasu 15 suka rasa rayukansu a Talata Mafara.

A Jihar Borno, an ruwaito kashe manoma 11 a ƙauyen Kuwawu, yayin da aƙalla mutum 20 suka mutu a Bokkos da ke Jihar Filato. A Jihar Neja kuma, mutum 42 suka mutu a wani hari da makiyaya suka kai a Ƙaramar Hukumar Rafi.

Hare-haren sun faru ne a yankuna daban-daban na ƙasar, kuma ana danganta su da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai daban-daban, ciki har da ɓarayin daji, 'yan ta'addan Daesh da sauran masu aikata laifuka da ke kai hare-hare a yankunan karkara.

A lokuta da dama, manoma ne ake kai wa hari yayin da suke aiki a gonakinsu ko girbin amfanin gona ko kuma a hanyarsu ta zuwa ko dawowa daga gonaki.

Masana harkokin tsaro sun ce hare-haren da ake ci gaba da kaiwa ba wai kawai suna salwantar da rayuka ba ne, amma suna kawo cikas ga harkokin noma, suna hana mutane komawa gona, tare da yin barazana ga samar da abinci a ƙasar da miliyoyin mutane ke dogaro da noma domin samun abin rayuwa.

Wadannan hare-hare na zuwa ne a muhimmin lokaci na damina, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar raguwar amfanin gona, tashin farashin kayan abinci da kuma tsananta halin ƙuncin rayuwa a al'ummomin da tuni suke cikin mawuyacin hali.

Duk da cewa jami’an tsaro sun ƙara kaimi wajen kai hare-hare kan ‘yanta’dda a sassa daban-daban na ƙasar, jama’ar karkara da shugabanninsu na ci gaba da kira da a ɗauki ƙarin matakai masu ƙarfi domin kare al'ummomin manoma da tabbatar da cewa mutane za su iya komawa gonakinsu cikin aminci.

Ga al'ummomi da dama na karkara, damar yin noma ba tare da fargaba ba na ƙara zama mai wahala, abin da ke nuna irin babbar barazanar da rashin tsaro ke yi ga tattalin arzikin Nijeriya, wadatar abinci da kuma zaman lafiyar al'umma baki ɗaya.