| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
An gudanar da zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su a jihar Neja
Masu zanga-zangar, daga ƙauyen Dekara da al'ummomin da ke makwabtaka da su a karamar hukumar Borgu sun taru a hedikwatar gwamnatin yankin da ke New Bussa don neman a saƙi wadanda aka yi garkuwa da su.
An gudanar da zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su a jihar Neja
Al'ummoni a jihar Neja sun yi Zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su a jihar

Al’umma jihar Neja da ke yankin Arewa maso tsakiyar Nijeriya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin 22 ga Satumba don kira ga gwamnati kan daruruwan mutanen da suka ce suna hannun ‘yanbindiga wata ɗaya bayan da aka yi garkuwa da su.

Harin da ‘yanbindigar suka kai kan al'ummomi da dama a Jihar na ɗaya daga cikin manyan satar mutane da aka taba yi a Nijeriya.

Masu zanga-zangar, daga ƙauyen Dekara da al'ummomin da ke makwabtaka da su a karamar hukumar Borgu inda suka ce ‘yanbindiga sun sace mutane kusan 600, wadanda galibinsu mata da yara da kuma tsofaffi ne, sun taru a hedikwatar gwamnatin yankin da ke New Bussa don neman a saki waɗanda aka yi garkuwa da su.

Borgu na da nisan kilomita 300 (mil 186) daga babban birnin jihar Minna, kana daga Yamma yana kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Benin.

Zanga-zangar ta ƙara matsin lamba ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu don magance matsalar rashin tsaro a ƙasar, lamarin da zama babban batu da ya fi mayar da hankali gabanin babban zaɓen Nijeriya a Janairun 2027.

Ko da yake Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a yi gaggawar ceto mutanen da aka sace bayan hare-haren na ranar 21 ga Agusta, sai dai har yanzu ba a kai ga gano su ba. "An tura hukumomin tsaro, amma har yanzu ba mu samu amsa daga gare su ba.

Gwamnati tana ƙoƙarin ceto mutanen," kamar yadda Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja Obed Nuhu Nana ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.

Kusan mutane 700 aka yi a garkuwa da su’

Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yanbinduga sun yi garkuwa da mutane fiya da 600, adadin da hukumomi ba su tabbatar ba kawo yanzu.

Abdullahi Yahaya Sadauki, shugaban ƙungiyar ci gaban matasa ta Karamar Hukumar Borgu, ya ce al'ummomi yankin sun kiyasta cewa kusan mutane 700 ne suke hannun masu garkuwa da mutane.

"A yi ƙidayar a ƙauyuka. Wannan ita ce hanya mafi kyau da za ta tabbatar ko ikirarinmu gaskiya ne ko a'a," in ji Sadauki.

Ko da yake kafar Reuters ba ta iya tabbatar da adadin ba da kanta.

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar kana memba a ƙungiyar mai suna Abdulmalib Dindey, ya ce rashin tsaro ya takaita zuwan mazauna yanki kasuwanni da duba lafiyarsu.

Hanifa Konkoso, mai shekaru 26, ta ce an rufe shaguna a Borgu duk da cewa ranar Litinin ce ranar kasuwa.

"Muna son gwamnati ta dauki mataki," in ji ta, inda ta kara da cewa mazauna yankin na ci gaba da matsa wa hukumomi lamba don tabbatar da sakin wadanda aka kama da kuma dawo da tsaro.

Rumbun Labarai
An tsare kwamandan NSCDC da wasu jami'an hukumar na jihar Neja kan mutuwar masu haƙar ma'adinai 37
Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitin mutum 10 don binciken mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC a Neja
Waɗanda suka tsira a Jihar Neja sun bayyana yadda abokan sana'arsu suka rasu a ɗakin da aka tsare su
Ana zargin giya ta kashe mutum 49 a Jihar Ondo da ke kudancin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kwamandan NSCDC bisa mutuwar masu haƙar ma'adinai 37 a jihar Neja
Majalisar Wakilan Nijeriya ta aika da ƙudirin kafa ’yansandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Dakarun Nijeriya sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi
Rundunar sojin Nijeriya 'ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya'
Samun ɗa namiji magaji ba ya gabana - Aliko Dangote
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar kai hare-hare makarantu da wuraren ibada
Ana zargin ‘yanta’adda da kashe aƙalla mutum 13 a wasu hare-hare a Jihar Filato ta Nijeriya
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 262, sun kuma ceto 27 da aka yi garkuwa da su
An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya