Ɗalibai 50 cikin fiye da 300 da aka sace daga makarantar St. Mary a Jihar Neja sun tsere - CAN
A cikin wata sabuwar sanarwa da ƙungiyar ta CAN ta fitar a ranar Lahadi, ɗalibai 50 ɗin da suka sun riga sun haɗu da iyalansu.
Ɗalibai hamsin da aka sace daga Makarantar Sakandare da Firamare ta St. Mary’s da ke Papiri, a Karamar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, sun tsere daga hannun masu garkuwa da su.
’Yan bindiga sun kai hari a makarantar cikin daren Juma’a, inda suka harbi mai gadi sannan suka yi awon gaba da fiye da dalibai 200, tare da malamai 13 da ma’aikatan da ba na koyarwa ba.
A cikin rahotonsa na farko game da lamarin, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) a Jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ma mai makarantar ne, ya ce an sace ɗalibai 215 tare da ma’aikata 12.
Amma zuwa ranar Asabar, ya ce dalibai 88 ba a san inda suke ba.
Sai dai a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa, Daniel Atori, ya fitar a madadinsa a ranar Lahadi, Faston ya bayyana cewa ɗaliban da suka tsere a ranar Asabar sun riga sun haɗu da iyalansu.
“Wannan sanarwa ce ga jama’a cewa a ranar Lahadi, 23 ga Nuwamban 2025, mun samu labari mai daɗi cewa dalibai hamsin sun tsere kuma sun koma wurin iyayensu,” in ji sanarwar.
Rev. Yohanna ya ce makarantar tana gudanar da tsarin kwana da na jeka-ka-dawo.
A cewarsa, sashen firamare na da ɗalibai 430, inda 377 ke kwana a makaranta, 53 kuma masu ‘yan jeka-ka-dawo.
Yayin bayani kan waɗanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba, ya bayyana:
“Yanzu haka, baya ga ɗalibai 50 da suka tsere suka kuma koma gida, muna da dalibai 141 da ba a sace su ba. A halin da muke ciki yanzu, ɗalibai 236, da yara uku na ma’aikata da ɗalibai 14 na sakandare da ma’aikata 12 suna nan a hannun masu garkuwa da su.”