Aƙalla mutane 23, ciki har da yara uku, aka kashe a ranar Talata sakamakon hare-hare uku daban-daban da aka ɗora alhakinsu kan 'ya ta'adda da ƙungiyoyin masu aikata laifuka a arewa maso gabashi da arewa maso yammacin Nijeriya, a cewar wani rahoto.
Wasu 'yanta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutum 11 a wani hari da suka kai a wani ƙauye a arewa maso gabashin jihar Borno, yayin da wasu 12 suka mutu a hare-haren da aka kai a ƙauyuka biyu a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya, a cewar rahotanni guda biyu da jami’an tsaro suka fitar.
Wasu 'yanta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne a kan babura da dama sun kai hari a al'ummar Pubago da ke gundumar Rumirgo a Borno a daren ranar Talata, a cewar ɗaya daga cikin rahotannin.
Rahoton ya ce har yanzu ba a ga wasu mazauna yankin ba, yana mai gargadin cewa adadin zai iya karuwa.
Hare-Hare daban-daban
A wasu hare-hare daban-daban a rana guda, 'yan bindiga sun kai hari a kauyukan Rumbuki da Nikai a gundumar Bukkuyum ta jihar Zamfara, in ji wani rahoton.
Maharan da ke kan babura da dama, sun kai hari a Rumbuki, "sun kashe mutane tara tare da raunata wasu mazauna takwas", inda wasu mutanen da dama suka bace, rahoton ya bayyana.
Sun kashe akalla "yara uku" a harin da aka kai a kauyen Nikai.
Ƙaruwar haɗin gwiwar 'yan bindiga da 'yan ta'adda ya zama abin damuwa ga hukumomi da masu sharhi.
Sojoji sun ce sun himmatu wajen kakkaɓe 'yan ta'adda da 'yan fashi a yankunan.
A cikin 'yan kwanakin nan 'yanta'addar Boko Haram, sun tsananta kai hare-hare kan sansanonin soji da al'ummomi a arewa maso gabas, wanda ya haifar da asarar fararen-hula da sojoji ciki har da manyan kwamandojin soji.
'Yanbindiga sun ci gaba da kai hare-hare a ƙauyuka, suna kashe mazauna, sace mutane don neman fansa da kuma wawushe kayan da ke cikin gidaje kafin su ƙona su.
Sojojin Nijeriya sun ce har yanzu suna jajircewa wajen kakkaɓe 'yanta'adda da 'yanfashi a kasar.















