Turkiyya ta ƙaddamar da shirin jigilar kaya ta Saudiyya saboda rufe Mashigar Hormuz
Ministan cinikayyar Turkiyya Omer Bolat ya yi shelar cewa kayayyakin da ba su iya wucewa ta hanyar ruwa mai muhimmanci ba ana juya akalar su zuwa hanyoyin jigila na daban.
Turkiyya ta ƙaddamar da wata yarjejeniya ta jigila ta Saudiyya domin tabbatar da cewa kayayyaki na ci gaba zuwa ƙasashen yankin yayin tsaikon da aka samu a Mashigar ruwan Hormuz, kamar yadda ministan cinikayya Omer Bolat ya bayyana.
Da yake magana a wani biki a Ankara, Bolat ya bayyana cewa kayayyakin da ba su iya wucewa ta hanyar ruwan mai muhimmancin ba za a juya akalarsu zuwa wasu hanyoyin jigila na daban.
"Mun ƙulla yarjejeniyar jigilar kayayyaki ta Saudiyya. Da wannan yarjejeniyar, kayayyakin da ba za su iya wucewa ta Mashigar ruwan Hormuz ba za su ci gaba da kaiwa ƙasashe na yankin, wasu ta hanyar bututu wasu kuma ta jigila ta hanyar titi," in ji shi.
Bolat ya tabbatar da cewa an fara bayar da biza ta wucewa a ƙarƙashin yarjejeniyar, yana mai ƙarawa da cewa matakin zai taimaka wajen ci gaba da cinikayya a yankin ƙasashe Larabawa da ke gaɓar Teku.
Hanyoyi na daban
Da yake magana game da yaƙin da aka fara a ƙarshen watan Fabrairu da hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran, ya ce an rufe wuraren samun makamashi, lamarin da ya janyo tsaiko mai muni kan kayayyaki na mai da sinadirai da taki.
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin na aiki domin hana lalata ababen da suka jiɓinci tattalin arziki.
Ya ce Turkiyya ta samu muhimmin ci-gaba a harkar jigila kuma a halin yanzu tana da wani fanni da ƙimarsa ta kai dala biliyan 112 .
Game da harkar noma, Bolat ya ce Turkiyya tana da isassun kayayyaki kuma tana tsammanin samun amfanin gona a wannan shekarar wanda ba ta taɓa samun irinsa ba.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ta samar da isasshen taki tare da rage harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigowa da su domin hana matsalolin samunsu.