Trump ya ce Hamas za ta "ɗanɗana kuɗarta" idan nan da ɗan lokaci ba ta ajiye makamai ba

Trump na goyon bayan Netanyahu kan tattaunawa game da Gaza, amma ya ce Amurka da Isra’ila ba su cim ma yarjejeniya game da Gaɓar Yamma ba a yayin da ake matsa lamba kan tsagaita wuta.

By
Shugaban Amurka Trump ya ce ajje amakaman na da muhimmanci don matsawa mataki na gaba ana aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar. / Reuters / Reuters

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi barazana ga ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ce wa ko dai nan da ɗan lokaci ta ajiye makamai ko ta “ɗanɗana kuɗarta” kamar yadda wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ya tanada, yana mai cewa Isra’ila na sauke nauyinta na yarjejeniyar.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai na haɗin gwiwa tare da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a wajen hutun Mar-a-Laga na Trump da ke Florida, shugaban na Amurka ya ce ajiye makaman wani ɓangare ne na samun ci gaba a yarjejeniyar.

“Idan ba su ajiye makamai kamar yadda suka yarda za su yi ba, to za su ɗanɗana kuɗarsu,” in ji Trump.
“Dole su ajiye makamai a cikin ƙanƙanin lokaci.”

Trump ya fili ƙarara nuna goyon baya ga Neyanyahu da ke noƙewa don aiki da mataki na gaba na yarjejeniyar tsagaita wutar.

Batutuwan yankin

Tun da fari, Trump ya fara tarbar Netanyahu a Mar-a-Laga, yana mai cewa tattaunawarsu za ta mayar da hankali kan Gaza da kuma wasu batutuwan yankin da na ƙasa da ƙasa.

Wannan ne karo na biyar da Trump ke karbar bakuncin Netanyahu tun hayan dawowar sa Fadar White House shekara daya da ta wuce, kuma hakan ya zo a lokacin da ake ta tababa kan tsallaka wa ga mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

“Ina fata cikin sauri za mu shiga babi na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar,” in ji Trump, yana mai cewa an kusa fara sake gina Gaza matukar aka cim ma fahimtar juna.

Trump ya kuma tabo batun yankin inda ya ce zai yi magana da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan don duba yiwuwar kai sojojon Turkiyya Gaza a wani ɓangare na kai dakarun zaman lafiya na ƙasa da ƙasa yankin.

Saɓani game da Gaɓar Yamma da aka mamaye

Trump ya kuma bayyana bambancin ra’ayin da ake da shi tsakanin Washington da Tel Aviv game da Gaɓar Yamma da ke ƙarƙashin mamaya, yana mai cewa ɓangarorin biyu ba su amince 100 bisa 100 kan yankin ba.

“Mun tattauna, babbar tattaunawa, ta tsawon lokaci game da Gaɓar Yamma, kuma ba zan iya cewa mun amince dari bisa dari game da Gabar Yamma ba, amma za mu kai karshe,” yana mai kara wa da cewa za a fitar da sanarwa “a lokacin da ya dace”.

Da yake nuni ga Netanyahu, Trump ya ce “Zai yi abinda ya dace”.

Dakarun Isra’ila da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna sun kashe akalla Falasdinawa 1,103 a Gabar Yamma, cikin har da Birnin Kudus da aka mamaye, sun kuma jikkata kusan 11,000 tare da kama kimanin 21,000 tun 7 ga Oktoban 2023, kamar yadda alƙaluman Falasɗinawa suka nuna.