Bayan rashin nasara da Arsenal ta yi a hannun Manchester City ranar Lahadi da ta gabata, toshon kocin Arsenal kuma jami’a a hukumar ƙwallo ta duniya, FIFA, wato Arsene Wenger ya aika saƙon goyon baya ga tsohon kulob ɗinsa.
Shan kashi da ci 1-2 a hannun City ya zo wa Arsenal a matsayin rashin nasara ta huɗu a gasannin gida Ingila, kuma hakan ya kassara damarmakin koci Mikel Arteta na lashe kofi a bana.
A halin yanzu, Man City za ta iya ɗarewa saman teburi idan ta lashe kwantan wasanta da Burnley gobe Laraba. Hakan zai zo da babban mamaki ganin cewa Arsenal ce ta ja ragamar teburin Firimiya tsawon watanni.
Kafin samun komabaya a gasar Firimiya, kofin FA da na Carabao sun kuɓuce wa Arsenal, inda a yanzu damarsu ta taƙaita kan kofunan Firimiya da na Zakarun Turai.
Cibayan da Arsenal ta samu a yunƙurinta na ɗaga kofin Firimiya da ta jima ba ta lashe ba, ya motsa zukatan masoya ƙungiyar ciki har da Wenger, wanda ya taɓa riƙe kulob ɗin na tsawon kusan shekaru 22.
Tsohon kocin ɗan asalin Faransa ya miƙa saƙon goyon baya kan burin Arsenal, inda yake nuna amannarsa kan cewa Gunners za su jure wa mamayar da City ke niyyar yi wajen shan gabansu.
An ambato Arsene Wenger a wani taro yana cewa, “Na yi imanin Arsenal za ta lashe kofin [Firimiya]. Na yi imanin haka matuƙa… Manchester City ba za ta kammala wasanninta babu tangarɗa ba.”
A yanzu dai Arsenal ta mai da hankali kan wasanta da Newcastle ranar Asabar mai zuwa, ranar da Manchester City za ta buga wasan dab da ƙarshe na kofin FA tare da Southampton.








