| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Fidan ya yi gargadi kan amfani da Mashigar Teku ta Hormuz a matsayin makami a rikicin yankin
Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya yi gargadin cewa tangarda ga hanyar na yin barazana ga zaman lafiyar yankin da tattalin arzikin duniya.
Fidan ya yi gargadi kan amfani da Mashigar Teku ta Hormuz a matsayin makami a rikicin yankin
Fidan ya ce dole ne rikicin da ake ci gaba da yi a yankin Gulf ya zama bai janyo a manta da batun Gaza ba / AA / AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a ranar Talata ya ce ‘Kar Mashigar Teku ta Hormuz ta zama makami, yana mai gargadin cewa tangarda ga hanyar na yin barazana ga zaman lafiyar yankin da tattalin arzikin duniya.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Waje Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani a Doha, Fidan ya kuma ce ya zama lallai a tabbatar da tashin hankalin da ke ci gaba da faruwa a yankin Gulf "ba zai sa a manta da batun Gaza ba."

Ya kuma yi gargadin cewa fadadar Isra'ila na ci gaba da zama babbar barazana ga "kwanciyar hankali da tsaro" na yankin.

Al Thani ya ce Qatar da Turkiyya suna goyon bayan kokarin shiga tsakani na Pakistan da nufin kawo karshen yakin Amurka-Isra'ila kan Iran da kuma sake bude mashigar Hormuz, yana mai jaddada bukatar dawo da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da 'yancin zirga-zirga ta hanyar mai matukar muhimmanci.

"Qatar da Turkiyya sun goyi bayan kokarin shiga tsakani na Pakistan don kawo karshen yaki kan ran da sake bude mashigar teku ta Hormuz," in ji shi.

Ministan Harkokin wajen Qatar ya kuma ce bai kamata Tehran ta yi amfani da hanyar ruwa a matsayin hanyar "zalunci ko cin zarafi" ga kasashen Gulf ba.

Da yake jawabi kan Gaza, Al Thani ya zargi Isra'ila da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma "amfani da tallafin jinkai a matsayin makami" a yankin.

An yi taron manema labarai na hadin gwiwa a yayin ziyarar aiki da Fidan ya kai Doha babban birnin Qatar.