An harbe wani ɗan majalisar jam'iyyar adawa a Sudan ta Kudu

Mutane hudu ɗauke da makamai sun mamaye gidan Luka Mathen Toupiny inda suka bindige ɗan majalisar har lahira a gidansa da ke Juba babban birnin ƙasar.

By
Luka Mathen Toupiny shi ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Cueibet a Majalisar Wakilan Sudan ta Kudu / Others

An bindige wani ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar adawa daga Sudan ta Kudu a gidansa da ke Juba babban birnin ƙasar.

Mutane hudu ɗauke da makamai sun mamaye gidan Luka Mathen Toupiny Luk a Gudele da misalin karfe 10 na dare a ranar Asabar inda suka bindige ɗan majalisar har lahira, in ji matarsa, Nyan Akolde a tattaunawarta da kafar watsa labarai ta Sudan Post a ranar Lahadi.

Gudele na yammacin Juba.

Akolde ta ce ɗan majalisar ya dawo gida ne daga addu’o’in dare a lokacin da harin ya faru. An kai Mathen asibiti cikin mawuyacin hali, amma ya rasu bayan awa guda sakamakon raunukan da aka masa, kamar yadda ta ƙara da cewa.

A cewar Akolde, an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a harbin mijinta, yayin da sauran biyu har yanzu ba a kama su ba.

Babu dalili

Har yanzu ba a san abin da ya haddasa kisan Mathen ba.

Mathen ya wakilci Ƙaramar Hukumar Cueibet a Majalisar Jihohi (Council of States), Babbar Majalisar Tarayya ta Sudan ta Kudu. Cueibet tana cikin jihar Lakes a tsakiyar Sudan ta Kudu.

Matten, wanda tsohon akawu ne na kotu, an zaɓe shi a Majalisar Wakilai a shekarar 2018 bayan rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Sudan ta Kudu.

Ya shiga majalisar karkashin tikitin Other Political Parties (OPP), wata kungiya da ke da alaka da jam'iyyun adawa.

‘Yan adawa na neman adalci

Babbar jam'iyyar adawa, SPLM-IO, karkashin jagorancin wanda aka dakatar, Mataimakin Firaminista Riek Machar, ta bukaci hukumomi su gudanar da bincike kan mutuwar Mathen kuma su gurfanar da waɗanda suka kashe shi gaban shari'a.

An san Mathen da gudummawarsa a kwamitin ilimi na majalisa da kuma rikon amana wajen shugabancin ƙasa, in ji dan majalisar SPLM-IO, Juol Nhomngek Daniel, a tattaunawarsa da Sudan Post a ranar Lahadi.

Hukumar 'yan sanda ta Sudan ta Kudu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba a lokacin da aka wallafa wannan labarin.