Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da yi wa Kiristoci kisan kare dangi - Sheik Bala Lau

A wata hira ta musamman da TRT Afrika Hausa, Sheik Lau ya ce bai kamata Amurka a matsayinta na babbar kasa mai fada-a-ji ta yi barazanar daukar irin wannan mataki ba tare da yin sahihin bincike kan lamarin ba.

Sheik Bala Lau, JIBWIS

Shugaban Kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah ta Nijeriya, JIBWIS, Sheik Abdullahi Bala Lau ya ce ga alama akwai wata ajanda da Amurka ke shiryawa a kan Nijeriya, shi ya sa take son fakewa da zargin ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi don shigar da sojojinta kasar.

Shugaban na JIBWIS ya fadi hakan ne a matsayin martani ga dambarwa da ke faruwa a tsakanin Nijeriya da Amurka bayan da Trump ya yi ikararin shiga Nijeriya don “ceton Kiristocin” da suka kai korafi Amurka cewa ana kasha su a Nijeriyar.

A wata hira ta musamman da TRT Afrika Hausa, Sheik Lau ya ce bai kamata Amurka a matsayinta na babbar kasa mai fada-a-ji ta yi barazanar daukar irin wannan mataki ba tare da yin sahihin bincike kan lamarin ba.

“Ai idan ma akwai wadanda ake kashewa a Nijeriya to lallai Musulmai ne suka fi yawa, duba ga jihohi irinsu Zamfara, Katsina, Sokoto, Neja, Kaduna, Borno, da Yobe da suka fi ko ina fuskantar matsalar ‘yan bindiga da ta Boko Haram,” in ji babban jigo na addinin Musuluncin a Nijeriya.

Wata kungiyar Kiristoci daga Nijeriya ce ta kai korafi da zargin cewa ana musu kisan gilla a Nijeriya, lamarin da ya jawo masu fada-a-ji da dama a Amurka suka yi ta mayar da martini da shan alwashin Amurka za ta shiga Nijeriya don cetonsu.

Sai dai masana da kwararru na ta sharhi cewa wannan wani salo ne na mamaya da Amurka ta dade tana amfani da shi a kan kasashe da dama kamar su Libiya da Syria da Iraki, inda ta shiga da nufin ceton ‘yan kasar amma sai ta bige da tarwatsa kasashen da sace albarkatun kasarsu.

Sannan a hannu guda, Shugaban JIBWIS ya ce su ma a bangaren Musulmai sun sha kai korafi ga Amurka kan kisan da ake yi wa mabiyan addinin a Nijeriya, amma ba ta taba daukar wani mataki makamancin wannan ba.

“Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Abuabakar ya taba tura da wakilai zuwa kasar Amurka da alkaluma kan abin da ke faruwa ga Musulmai. Suna da wannan labari.

“Ni kaina ina cikin wasu wakilai da suka je Amurka kamar shekaru takwas da suka wuce, a kan abubuwan da ya kamata gwamnatin Amurka ta sani,” ya ce.

A cikin korafin da Kirisotcin suka kai Amurka har da batun cewa ana so a mayar da Nijeriya kasar Musulunci ta hanyar dabbaka shari’a, amma Sheik Bala Lau ya ce ba Nijeriya gaba daya ake son dabbaka shari’a ba, wasu jihohin kasar ne masu yawan mabiya Musulmai ke yin hakan.

“Kundin tsarin Mulkin Nijeriya ya bai wa kowa ’yancin ya yi addininsa. Tun da ba Nijeriya ba duk kasashen duniya kowa ya ba ka tsarin ka yi addininka. Saboda haka a matsayina na Musulmi da nake addini kuma mafi rinjayen inda muke zaune Musulmi ne, me zai hana mu yi shari’a? Tun da dokar kasarmu ta ba mu dama mu yi addini.

“Idan ya ce (Shi Trump) me ya sa suke yin shari’ar Musulunci ko za su yi shari’ar Musulunci? Mece ce alakarsa da kasar Saudiyya da mafi yawansu Musulmi ne kuma suke shari’ar Musulunci kuma yake kawance da su? Kuma sannan da yake yana da abin da yake samu a wajensu su yin shari’ar Musuluncin yanzu ba laifi ba ne, amma Musulmin da yake Nijeriya shi ne idan ya yi shari’ar Musulunci ya yi laifi.”