Abin da muka sani kan yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta mako mai zuwa
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Abin da muka sani kan yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta mako mai zuwaIsra'ila ta kuma ba da haske cewa sakamakon yaƙinta da Iran ya ba da damar yiwuwar ci gaba da tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙi.
Mourners react near the body of a Palestinian killed in an Israeli strike, in Gaza City / Reuters

Fatan samun tsagaita wuta a Gaza ya karu bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana sa ran cim ma yarjejeniya “cikin mako mai zuwa.”

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi nuni a ranar Lahadi da cewa akwai “damar da aka samu” daga yaƙin kwanaki 12 da aka yi da Iran, wanda zai iya kawo ƙarshen hare-haren bama-baman da Tel Aviv ke yi a yankin Falasɗinawa da aka mamaye.

Maganganun shugabannin biyu sun haifar da hasashe kan yiwuwar samun ci gaba a tattaunawar sirri don kawo ƙarshen yaƙin Gaza, wanda ya hallaka mutum 56,500 tun watan Oktoban 2023.

Yunƙurin tsagaita wuta da dama sun kasa kawo zaman lafiya a Gaza, inda Isra’ila ta jefa bama-bamai da suka kai yawan bama-baman Hiroshima guda shida a cikin watanni 20 da suka gabata.

Me Isra’ila ke cewa?

A wata ziyara da ya kai ga hukumar leƙen asirin cikin gida ta Isra’ila, Shin Bet, a ranar Lahadi, Netanyahu ya ce: “Ina so in sanar da ku cewa kamar yadda kuka sani, damarmaki da dama sun buɗe a yanzu bayan wannan nasara.”

Maganganunsa sun zo ne jim kadan bayan babban hafsan sojin Isra’ila, Laftanar Janar Eyal Zamir, ya ce yaƙin da aka yi da Iran, wanda ya ƙare a ranar 24 ga Yuni, na iya “taimakawa wajen cim ma burin Isra’ila a Gaza.”

Kwamitin tsaron Isra’ila zai gana a ranar Litinin. Ron Dermer, wanda ke kusa da Netanyahu kuma a halin yanzu yana matsayin ministan harkokin dabarun Isra’ila, ana sa ran zai gudanar da tattaunawar tsagaita wuta a ranar Litinin a Fadar White House, kamar yadda kafafen watsa labarai na Isra’ila suka ruwaito.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta ruwaito cewa kalaman Netanyahu na baya bayan nan cewa ceto mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza ya zama babban fifiko, maimakon maimaita burinsa na “kawo ƙarshen Hamas,” ya nuna sauyi a manufofinsa.

Isra’ila nawa ne ake garkuwa da su a Gaza?

Hamas ta ɗauki mutum 251 zuwa Gaza yayin wani hari da ta kai Isra’ila a ranar 7 ga Oktoban 2023.

An saki fiye da mutum 100 a ƙarshen 2023, ciki har da Isra’ilawa 78 da aka saki a yarjejeniyar musayar mutane da kuma baƙi 27 da ke da ‘yan kasa biyu da aka saki ba tare da yarjejeniya ba.

Mutane takwas an sake su sakamakon hare-haren sojin Isra’ila yayin da Hamas ta saki mata hudu bisa dalilan jin kai. Adadin wadanda aka tabbatar sun mutu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya kai 82.

A yanzu haka, mutum 23 ne suka rage da ake garkuwa da su a Gaza.

Me Amurka ke so?

Amurka tare da masu shiga tsakani daga Masar da Qatar sun gabatar da shawarar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 60 wadda za ta haɗa da sakin rabin mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su a musayar Falasdinawa da kuma gawarwakin wasu Falasdinawa.

A karkashin wannan yarjejeniya, Hamas za ta saki sauran wadanda aka yi garkuwa da su idan aka cim ma tsagaita wuta ta dindindin. Shawarar ta kuma buƙaci a gaggauta shigar da tallafin jinƙai zuwa yankin da aka killace.

A ranar 28 ga watan Yuni Shugaba Trump ya ce Netanyahu yana tattaunawa “a yanzu” da Hamas kan yarjejeniya.

“Ku kulla yarjejeniya a Gaza, ku dawo da wadanda aka yi garkuwa da su,” Trump ya wallafa a dandalin Truth Social a safiyar ranar 29 ga Yuni.

Hamas na neman tsagaita wuta

Wani jami’in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun sanar da masu shiga tsakani game da shirinsu na ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta.

Sai dai, Hamas ta sake jaddada buƙatunta cewa duk wata yarjejeniya dole ne ta kawo ƙarshen yaƙin tare da tabbatar da janyewar Isra’ila daga yankin bakin teku, inda Isra’ila ta lalata kashi 92 cikin 100 na dukkan gine-gine tun watan Oktoban 2023.

Isra’ila ta ce za ta iya kawo karshen yakin ne kawai idan Hamas ta “miƙa makamanta kuma ta rushe.” Hamas ta ƙi amincewa da ajiye makamanta.

Gaza na cikin mawuyacin hali na jinƙai yayin da Isra’ila ta kashe ɗaruruwan Falasdinawa yayin da suke neman abinci a cibiyoyin tallafi.