Akalla mutane 20 ne aka kashe bayan wasu ’yanbindiga da ke kan babura sun kai hari wani ƙauye a yankin karkara na Jihar Taraba, da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Waɗanda suka tsira daga harin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Asabar cewa maharan sun buɗe wuta a ƙauyen Binnari jim kaɗan bayan Sallar Jumma’a, lamarin da ya sa mazauna ƙauyen suka tsere zuwa wurare daban-daban domin neman mafaka.
“Mutane suna gudu ta hanyoyi daban-daban domin tsira daga harin. Babu wanda ya san inda zai je domin ya tsira,” in ji wani mazaunin ƙauyen mai suna Isiyaku Musa.
Wani mazaunin ƙauyen, Sa’idu Nuhu, ya ce an ƙirga gawawwaki fiye da 20 bayan maharan sun bar wurin, yana mai cewa har yanzu ba a gano wasu mutane ba.
Sai dai rundunar ’yansanda ta bayyana adadin waɗanda aka kashe da ya fi ƙasa da wannan, inda ta ce an gano gawawwaki 10 zuwa yammacin ranar Jumma’a.
Shugaban al’umma, Malam Abubakar Saifullahi, ya ce maharan sun iso ne a kan babura kusan 50, inda kowanne babur ke ɗauke da mutum biyu, kafin su fara kai harin.
Ya ce sun yi wa shaguna fashi, inda suka sace kuɗi, abinci da sauran kayayyaki. Haka kuma, sun kwashe baburan da mazauna ƙauyen suka bari yayin da suke tserewa daga tashin hankalin.
Jihar Taraba, wadda ke yankin arewa maso gabashin Nijeriya, ta sha fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke ɗauke da makamai, waɗanda aka fi sani da ’yanbindiga. Waɗannan ƙungiyoyi suna kai hare-hare kan al’ummomi, yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, tare da karɓar kuɗaɗen haraji ba bisa ƙa’ida ba daga manoma da masu haƙar ma’adanai a yankunan da ke da nisa.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta yi Allah wadai da harin, inda ta zargi hukumomi da barin al’ummomin karkara cikin yanayin da ke sa su zama cikin rauni ta yadda za a iya kai musu hari a ko yaushe.
“Rashin nasarar da hukumomi ke ci gaba da yi wajen gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan gaban shari’a a fili yana ƙara ƙarfafa masu aikata laifuka su ci gaba da aikata su ba tare da fargaba ba,” in ji ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama a shafukan sada zumunta.
Ayyukan ’yanbindiga na ƙara zama babbar barazana ga al’ummomi a faɗin arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya. A waɗannan yankuna, ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai waɗanda galibi kuɗi ne ke tunzura su suna gudanar da ayyukansu a yankunan da ke da nisa, inda a lokuta da dama suke rinjayar jami’an tsaro.
A wani labari na daban, rundunar sojin Nijeriya a ranar Asabar ta bayyana cewa ta kashe wasu mutane 15 da ake zargin ’yanta’adda ne a wani samamen hari ta sama da ta kai a Jihar Borno, da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

















