| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Jakadan Nijeriya a Indiya, Ambasada Saidu Muhammad ya gana da ’yan Nijeriya 198 da ke tsare a lokacin ziyararsa zuwa kurkuku daban-daban a faɗin Indiya.
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Muhammad ya ce an gudanar da ziyarorin ne domin fahimtar halin da ’yan Nijeriya da ake tsare da su a Indiya suke ciki da kuma damuwarsu.

Jakadan Nijeriya a Indiya, Ambasada Saidu Muhammad, ya ce ya gana kai-tsaye da ’yan Nijeriya 198 da ke tsare a lokacin ziyararsa zuwa kurkuku daban-daban a faɗin Indiya, a wani mataki na ƙarfafa abin da ya bayyana a matsayin diflomasiyyar da ta mayar da hankali kan ɗan ƙasa.

A yayin wata ganawa da ’yan jaridun diflomasiyya a New Delhi, inda ’yan jarida suka taru domin ɗaukar rahotannin taron ƙasashen BRICS na shekarar 2026, Muhammad ya ce an gudanar da ziyarorin ne domin fahimtar halin da ’yan Nijeriya da ake tsare da su a Indiya suke ciki da kuma damuwarsu.

A cewar jakadan, ya ziyarci kurkuku da dama, ciki har da waɗanda ke ɗauke da fursunonin Nijeriya 16, fiye da 70 da kuma fiye da 50, da kuma mata da ’yan mata 19 da ake tsare da su. Gaba ɗaya, tawagar ta gana kai tsaye da ’yan Nijeriya 198 cikin tsawon kwanaki uku.

 “Wannan ya nuna cewa gwamnatinmu ta damu da ’yan ƙasarta ne. Muna kiran hakan diflomasiyyar da ta mayar da hankali kan ɗan ƙasa,” in ji Muhammad.

Zargin cin zarafin fursunoni a Indiya

Ya bayyana cewa a yayin ziyarorin, mutanen da ake tsare da su sun bayyana damuwa kan batutuwa da suka haɗa da zargin cin zarafi da wariyar launin fata, da ƙarancin samun wakilcin lauyoyi, jinkirin gudanar da shari’o’i da kuma rashin isasshiyar kulawar lafiya.

Jakadan ya ce nan take ya tattauna batutuwan da aka gabatar da su da hukumomin gidajen yari, inda ya gano cewa yawancin ƙalubalen sun samo asali ne daga tsawaita bincike da jinkiri a tsarin shari’a, ba wai daga halayen jami’an gidan yari ba.

“Mun fahimci cewa jami’an gidan yari gabaɗaya suna ba da haɗin kai, amma yawancin mutanen da ake tsare da su suna jiran shari’a ne, kuma tsarin shari’a yana ɗaukar lokaci,” in ji shi.

Muhammad ya jaddada cewa tawagar ta yi ƙoƙarin rage gibin sadarwa ta hanyar tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa tare da kare haƙƙoƙin ’yan Nijeriya.

Ya kuma jaddada cewa ko da kuwa wane irin zargi ake yi wa mutanen da ake tsare da su, dole ne a mutunta haƙƙoƙinsu na ɗan’adam na asali.