Kotu ta ba wa NDLEA damar tsare jirgin ruwa da ma’aikatansa 21 kan dakon hodar ibilis daga Brazil
Jami'an NDLEA, wadanda suka yi aiki bisa ga sahihan bayanan sirri, sun gano hodar iblis da aka ɓoye a cikin ramin jirgin a ranar 6 ga Disamban 2025, a cewar sanarwar hukumar a ranar Laraba.
Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Lagos ta ba da umarnin tsare wani jirgin ruwan dakon kaya, da matuƙinsa da sauran ma’aikatansa 20 bayan kama hodar iblis har kilogiram 25.5 a cikinsa a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa.
Umarnin ya biyo bayan wata takardar neman izini da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta shigar ne bayan jami'an hukumar sun gano hodar iblis din a cikin jirgin ruwan 'yankasuwa, MV San Antonio, wanda ya isa Nijeriya daga Brazil.
Jami'an NDLEA, wadanda suka yi aiki bisa ga sahihan bayanan sirri, sun gano hodar iblis da aka ɓoye a cikin ramin jirgin a ranar 6 ga Disamban 2025, a cewar sanarwar hukumar a ranar Laraba.
Bayan da jirgin ya sauke kayansa gaba daya, an kama ma'aikatansa guda 21 waɗanda suka haɗa ‘yan kasashe daban-daban - ciki har da Rasha da Philippine da Ukraine da Azerbaijan - tare da miyagun ƙwayoyin da aka kama.
Wannan ci gaban ya zo ne makonni kadan bayan jami'an NDLEA sun kama wani jirgin ruwan, MV Nord Bosporus, wanda shi ma daga tashar jiragen ruwa ta Santos na Brazil ya taso, ɗauke da kusan kilo 20 na hodar iblis da aka ɓoye a ƙarƙashin kayansa a tashar Tekun Apapa a ranar 16 ga Nuwamban 2025.
Bisa la’akari da ƙa'idojin shari'a na duniya, NDLEA a ranar Jumma'a, 12 ga Disamban 2025, ta shigar da ƙara mai lamba FHC/L/MISC/1408/2025 a gaban Mai Shari’a Friday Nkemakonam Ogazi, tana neman umarnin a tsare jirgin da ma'aikatan jirgin har sai an kammala bincike da kuma shigar da ƙara.
Da yake yanke hukunci kan buƙatar, Alkali Ogazi ya amince da buƙatar kuma ya ba da umarnin tsare jirgin MV San Antonio da ma'aikatansa na tsawon kwanaki 14 da farko.
“An umarci kotu ta tsawaita tsare jirgin ruwan MV San Antonio wanda mai shigar da ƙara, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ke yi bincike a kai, na tsawon kwanaki 14 a shari’ar farko bayan kama kilogiram 25.5 na hodar iblis a cikin jirgin a ranar 6 ga Disamban 2025 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, har sai an kammala bincike da ko shigar da ƙarar laifuka da kuma gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji alkalin.
Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 29 ga Disamban 2025.
Da yake mayar da martani ga wannan ci gaba, Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce ƙwace kayan ya sake tabbatar da ƙudirin hukumar na hana kungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa da kuma abokan aikinsu na gida samun wani matsayi a Nijeriya.
Ya yaba wa jami'an rundunar dabarun Apapa bisa nasarar da suka samu a jere, yana mai bayyana su a matsayin shaida na ƙaruwar karfin hukumar da kuma ƙudurinta na wargaza hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi da ke fakon Nijeriya da kuma yankin Afirka ta Yamma.
Marwa ya kara da cewa NDLEA za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da abokan hulda na gida da na waje don tabbatar da cewa ba za a iya jure shan miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi ba a kasar.