Hukumar ƙididdiga ta Ghana, a ranar Laraba ta ce hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ƙaru a wata na uku a jere zuwa watan Yuni, inda ta kai kashi 5.3 cikin 100 a cikin shekara ɗaya daga kashi 3.7 cikin 100 a watan Mayu.
Masanin ƙididdiga na gwamnati Alhassan Iddrisu ya danganta ƙaruwar farashin kan kayayyaki da ba na abinci ba, ciki har da sufuri, gidaje, da fannin ilimi.
Hauhawar farashin kayayyakin ta kasance ƙasa da kashi 13.7 cikin 100 a irin wannan wata a bara, in ji Iddrisu yana mai ƙari da cewa an ƙara samun matsi na farashin kayayaki.
Ƙasar da ta yi fice wajen samar da zinare da man fetur da koko, ta fara fita daga mummunan yanayin matsin tattalin arziki da ta faɗa a cikin shekaru da dama.
'Ta cancanci sa ido sosai'
"Ƙaruwar farashin kayayyaki da aka samu a kwanan nan ta cancanci sa ido sosai don tabbatar da nasarorin da aka samu a baya," kamar yadda Idrissu ya shaida wa manema labarai.
Kazalika Hukumar ƙididdiga ta Ghana ta ce kayayyakin da ake samarwa a cikin gida sun ba da gudunmawar fiye da kashi 86 cikin 100 ga ƙaruwar farashin kayayyaki.
Babban Bankin Ghana na shirin ɗaukar mataki kan darajar riba da ake samu a ƙarshen wannan watan.
Ya dakatar da shirin zagayen rage darajar kuɗi a watan Mayu saboda damuwa kan hauhawar farashin kayayyaki.












