Shigar kuɗaɗe daga waje cikin Nijeriya don zuba jari ta ƙaru da kusan kashi 90% a 2025 – Hukumomi
Shigar kuɗaɗe daga wajen Nijeriya zuwa cikin ƙasar ya ƙaru zuwa kusan kashi 90% a shekarar 2025, sakamakon yadda mafi yawanci masu neman zuba jari daga ƙasashen waje suka ringa kai kuɗinsu kasuwannin hada-hadar kuɗi domin neman riba.
Shigar kuɗaɗe daga wajen Nijeriya zuwa cikin ƙasar ta ƙaru zuwa kusan kashi 90 a shekarar 2025, inda yawanci hakan ya samo asali daga masu neman zuba jari daga ƙasashen waje, inda suka kai kuɗinsu kasuwannin hada-hadar kuɗi domin neman riba, bayan gyare-gyaren tattalin arziki.
Bisa ga bayanan hukuma, jumallar jarin da aka zuba daga wajen ƙasar ya karu zuwa dala biliyan 23.22 daga dala biliyan 12.32 a 2024.
Ƙarin ya faru ne saboda ‘yan ƙasashen waje da suka zuba jari a kamfanonin cikin gida wanda ya tashi zuwa dala biliyan 19.74 daga dala biliyan 8.38, wanda ya kai kusan kashi 85% na jumullar jarin da aka shigar.
Daga cikin manyan rukunin zuba jari, zuba jari a sashen hada-hadar kuɗi ya ƙaru zuwa dala biliyan 13.83, yayin da shigar takardun lamuni ya kusan ninkawa sau biyar inda ya kai dala biliyan 4.89. Zuba hannun jari a kamfanoni ya ƙaru zuwa dala biliyan 2.10.
Sashen banki shi ne babban tushen shigowar jarin
A gefe guda, jarin kai-tsaye daga waje (FDI) ya karu ne kadan zuwa dala miliyan 923, daga $675 miliyan a 2024, abin da ke nuna ci gaba da taka‑tsantsan daga masu zuba jari game da sadaukarwar dogon lokaci.
Shigowar jarin da aka bayyana a matsayin “sauran rukunai na zuba jari”, ciki har da lamuni, sun fadi zuwa dala biliyan 2.55 daga dala biliyan 3.27. Sashen banki ne ya karɓi mafi yawan waɗannan shigowar kuɗin.
Masana suna cewa bayanan sun nuna masu zuba jari na ƙasashen waje sun ƙara yawan harkokin kasuwanci a Nijeriya, amma mafi yawansu don neman riba, abin da ke barin tattalin arzikin cikin haɗari idan aka samu sauye-sauyen yanayin harkokin kuɗi na duniya.