Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan wata doka da ta umarci tura duk kuɗaden mai da gas na gwamnati kai-tsaye cikin asusun gwamnati a wani gagarumin garambawul ga harkar kudin ƙasar.
Ya sanar da haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ranar Laraba.
A ƙarƙashin doka, kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL) na riƙe kashi 30 cikin 100 na ribar mai da gas domin sake gudanar da binciken neman mai a cikin ƙoramun cikin ƙasa.
A halin yanzu shugaban ƙasar ya ce za a riƙa saka kuɗin a cikin asusun gwamnatin tarayyara ƙasar ne inda gwamnatin za ta fitar da su domin a yi aikace-aikace.

Kazalika kamfanin NNPC na riƙe kashi 30 cikin 100 na cinikin mai da gas a matsayin kuɗin gudanarwa tare da karɓar kashi 30 cikin 100 daga kwangilolin samar da mai na haɗin gwiwa.
A ƙarƙashin sabon umarnin, dukkan kuɗaɗen shiga za su shiga asusun gwamnatin tarayya kai-tsaye.
Haraji kan ribar mai da sauran kuɗaden shiga waɗanda a da kamfanin kula da harkar haƙar mai (NUPRC) ne ke karɓar su za su wuce asusun gwamnatin tarayya kai-tsaye.
Kazalika hukumar NMDPRA mai kula da adana da dakon ɗanyen mai da kuma tace mai za ta miƙa duk kuɗaɗen da take samu, inda za a samar mata da kuɗin da take buƙata domin ayyukanta ta hanyar kasafin kudi.
Ofishin Tinubu ya ce cire kuɗaɗen da doka ta ba da damar yi ya rage kuɗaɗen shigar gwamnati sosai, ya kuma taka rawa ga rashin kuɗade ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da na ƙananan hukumomin ke fama da shi.
Shugaban ya kuma ba da umarnin sake nazari kan dokar tare da kafa wani kwamiti na aiwatarwa domin tabbatar da sauye-sauyen.











