Wata tambaya na buƙatar amsa a Kamaru. Shin ina Shugaba Paul Biya yake?
A tsawon fiye da shekara 40, shugaban mai shekaru 93 ne ke jagorantar ƙasar mai arziƙin man fetur Sai dai ‘yan Kamaru na ci gaba da nuna ƙarin damuwa a ‘yan makonnin nan a kan ƙin ganinsa a bainar jama’a.
Shugaba Biya shi ne shugaban ƙasar da ya fi tsufa a duniya inda ya bar ƙasarsa a ranar 7 ga Yuni a wani abu da jami’an ƙasar suka kira da “gajeren hutu a Turai” tare da matarsa Chantal Biya.
Gwamnatin ƙasar ba ta yi ƙarin bayani dangane da takamaimai ƙasar da ya tafi a Turai ba.
Sai dai shugaban na Kamaru ya rinƙa zuwa Switzerland akai-akai a shekarun da suka gabata, a wani lokacin domin duba lafiyarsa.
Ministan watsa labarai Rene Emmanuel Sadi a ranar 18 ga Yuni ya musanta cewa an kwantar da Biya asibiti a Geneva.
An yi wa Shugaba Biya ganin ƙarshe a bainar jama’a a ranar 20 ga watan Mayun 2026, a lokacin bikin Ranar Samun ‘Yancin Kamaru a birnin Yaounde
Waye jagora a yanzu?
Gwamnatin Kamaru ta haramta duk wani nau’i na tattaunawa a bainar jama’a game da lafiyar Paul Biya tun bayan da ya yi irin wannan tafiyar ta tsawon lokaci a shekarar 2024.
Sai dai wannan haramcin bai kashe bakin jama’a ba, musamman ‘yan adawa.
Jam'iyyar adawa ta Cameroon Democratic Union (UDC) ta bukaci hukumomi su bayar da "cikakken bayanin da ya dace kan yadda ake ci gaba da tafiyar da harkokin ƙasa yadda ya kamata." A lokaci guda, Mataimakin Shugaban wata jam’iyyar ta Cameroon Renaissance
Movement (MRC), Mamadou Mota, ya ce akwai "gagarumin giɓi a gwamnatin" ƙasar.
Sai dai bayan wani taron da ba kasafai ake yi ba na jam'iyyar da ke mulkin ƙasar ta Cameroon People’s Democratic Movement (CPDM), a ranar 22 ga Yuli, Sakataren Yaɗa Labaranta, Jacques Fame Ndongo, ya ce Shugaba Paul Biya na "bibiyar dukkan muhimman takardu da harkokin gwamnati cikin tsanaki" daga ƙasashen waje.
A Kamaru, babu wani tanadi da ke ba da dama ga Mataimakin Shugaban Ƙasa ya karɓi ragamar mulki kai-tsaye idan Shugaban Ƙasa ya yi tafiya ko kuma ya kasance ba ya cikin ƙasar na ɗan lokaci.
Idan Shugaban Ƙasa yana wajen ƙasar sannan duk da haka zai iya gudanar da aikinsa, zai iya ci gaba da mulki.
Ministoci ne ke gudanar da harkokin yau da kullum na ma'aikatunsu, yayin da Sakatare-Janar na Fadar Shugaban Ƙasa ke kula da takardu da sauran muhimman al'amura. Wannan shi ne abin da ke gudana a halin yanzu.
A farkon wannan shekarar, Kamaru ta dawo da muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda aka ake ganin zai iya karɓar mulki idan Shugaban Ƙasa ya rasu ko kuma ya zama ba zai iya ci gaba da gudanar da aikinsa ba. Sai dai har yanzu ba a naɗa wanda zai riƙe wannan muƙami ba.
Kafin ƙirƙirar muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya tanadi cewa Shugaban Majalisar Dattawa ne zai zama shugaban ƙasa na riƙo idan shugaban ƙasa ya rasu ko ya zama ba zai iya ci gaba da aiki ba, sannan dole ne a gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa cikin kwanaki 20 zuwa 120.
Shugaban Majalisar Dattawa na yanzu shi ne Aboubakary Abdoulaye, mai shekara 65, wanda aka zaɓa a watan Maris, bayan ya gaji Marcel Niat Njifenji, mai shekara 91.
Paul Biya ya hau karagar mulki a shekarar 1982 bayan murabus ɗin shugaban ƙasar na farko, Ahmadou Ahidjo.
A watan Oktoban 2025, Biya ya lashe wa'adi na takwas a matsayin Shugaban Ƙasa bayan zaɓen da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon abokin siyasarsa, Issa Tchiroma Bakary, ya yi watsi da sakamakonsa.
















