Barcelona za ta ƙwato Haaland daga Manchester City don maye gurbin Lewandowski

Yayin da ake ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin Barcelona, wani ɗan takara ya ce zai ɗauko zaƙaƙurin ɗanwasa Erling Haaland daga Manchester City idan ya ci zaɓe.

By
A halin yanzu, Erling Haaland yana da kwantiragi da Manchester City har zuwa 2034. / Reuters

Rahotannin daga Sifaniya na cewa, ɗan takarar shugabancin Barcelona Victor Font ya tuntuɓi Manchester City ta Ingila kan ɗauko gwarzon ɗanwasa Erling Haaland zuwa Barca.

Yayin da ake ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugabancin Barcelona, ‘yan takara biyu ne ke neman jagorancin ƙungiyar, wato Victor Font da kuma tsohon shugaban Barca, Joan Laporta.

Wakilan Font, wanda ake sa ran za su samu muƙami a Barca idan ya ci zaɓe, sun yi wani zama da shugabannin Manchester City don tattauna yiwuwar karɓo ɗaya cikin ‘yanwasa mafi tashe a duniya.

Carles Planchart da Xavier Aguilar sun tattauna a Madrid tare da Ferran Sorriano, shugaban gudanarwa na Manchester City, da kuma Hugo Viana, daraktan wasanni na City.

A ƙarshen kakar bana ne kwantiragin tauraron ɗanwasan Barca ɗan asalin Poland, Robert Lewandowski za ta ƙare, wato ranar 30 ga Yuli sakamakon cewa ba a sabunta masa kwantiragin ba.

Wannan dalili ne ya sa tawagar Victor Font ke fatan kawo Erling Haaland, duk da cewa ɗanwasan ɗan asalin Norway na da kwantiragi a Man City har zuwa 30 ga Yunin 2034.

Wasu masu sharhi na ganin wannan yunƙuri na fara fafutukar maye gurbin Lewandowski mai shakru 37, da Haaland mai shakeru 25, wata dabara ce ta neman ƙuri’a daga ɓangaren Font.

Shi ma a ɓangarensa, Joan Laporta an ambato shi a baya yana jaddada aniyarsa ta dawo da gwarzon tsohon ɗanwasan Barcelona, Lionel Messi, don cika burin tarin masoya ƙungiyar.