| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Jiragen dakon mai uku sun taka nakiyoyin da aka dasa a Mashigar Ruwan Hormuz
Ta ce tana sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin ba dare ba rana, inda ta yi gargaɗin cewa kashe na’urorin bin diddigin jiragen ruwa da shiga wuraren da aka hana zirga-zirga na iya janyo babban haɗari.
Jiragen dakon mai uku sun taka nakiyoyin da aka dasa a Mashigar Ruwan Hormuz
Jiragen dakon mai uku sun taka nakiyoyin da aka dasa a Mashigar Ruwan Hormuz / Reuters (Wire)

Rundunar sojin ruwan Iran ta ce wasu jiragen dakon mai uku sun taka nakiyoyin da aka dasa a ƙarƙashin ruwa, lamarin da ya haddasa tashin gobara a lokuta daban-daban a cikin mashigar ruwan Hormuz da kewayenta a ranar Litinin.

Sanarwar da gidan talabijin na ƙasar, IRIB, ya watsa ce ta bayyana hakan.

Rundunar sojin ruwan Iran ta ce wani jirgin dakon mai ya taka nakiya da sanyin safiyar Litinin a wani yanki da ke gabashin mashigar ruwan, wanda Iran ta ayyana a matsayin wurin da aka hana zirga-zirga. Lamarin ya haddasa gobara, tare da hana jirgin ci gaba da tafiya.

Ta ce tana sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin ba dare ba rana, inda ta yi gargaɗin cewa kashe na’urorin bin diddigin jiragen ruwa da shiga wuraren da aka hana zirga-zirga na iya janyo babban haɗari.

Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa masu mallakar jiragen ruwan da suka yi watsi da gargaɗin kan hanyoyin zirga-zirga za su ɗauki alhakin duk abin da ya biyo baya.

A wani labarin daban, rundunar sojin ruwan rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce wasu jiragen dakon mai biyu sun taka nakiyoyi yayin da suke ƙoƙarin wucewa ta kudancin mashigar ruwan Hormuz.

Sashen hulɗa da jama’a na rundunar ya yi zargin cewa jiragen na tafiya ne ƙarƙashin jagorancin jami’an sojin Amurka kai tsaye, tare da taimakon jiragen yaƙin ƙasar.

Ta ce fashe-fashe masu ƙarfi da dama sun afku a jiragen, inda haskensu ya mamaye sararin samaniyar mashigar ruwan na tsawon sa'o'i.

Sanarwar ta ce jiragen na kusa da wasu jiragen dakon mai biyu da suka fuskanci irin wannan lamari a baya, tana mai cewa jiragen dakon mai shida ne suka kama da wuta kuma suke nutsewa a mashigar ruwan tun daga ranar Lahadi.

Sai dai ba a bayyana ko wannan adadi ya haɗa da jirgin da rundunar sojin ruwan Iran ta sanar a baya ba.

Rundunar sojin ruwan IRGC ta kuma yi zargin cewa gurɓatar muhalli sakamakon fashe-fashen ta bazu a cikin ruwan mashigar da kuma gaɓar tekun.

Ta bayyana matakin a matsayin martani ga takunkumin killace tashoshin jiragen ruwan Iran da Amurka ta sanya, da kuma keta dokokin zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran.

Sanarwar ta ce: “An dasa nakiyoyi a hanyar kudancin mashigar ruwan Hormuz da Amurka ta ƙirƙira, inda aka mayar da ita tamkar katangar wuta.”

Ta kuma gargaɗi masu mallakar jiragen ruwa kan haɗa kai da sojin Amurka.

A lokuta da dama, dakarun Iran sun sha bayar da rahoton cewa jiragen dakon mai na taka nakiyoyi yayin da suke amfani da hanyoyin da Tehran ke cewa ba ta amince da su ba. Hakan na faruwa ne a yayin yaƙin da Amurka ke yi da Iran da kuma killace tashoshin jiragen ruwan ƙasar da Washington ta sanya.

A baya, rahotannin tantance bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa Iran ta dasa nakiyoyin yaƙin ruwa a mashigar ruwan a yayin rikicin da ake ciki.

Mashigar ruwan Hormuz tana haɗa Tekun Fasha da Tekun Oman, kuma tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da ake bi wajen jigilar man fetur a duniya.