Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin biyan kudin fansa don ceto daliban Jihar Neja

Sanarwar ta ce babu wani kudin fansa da aka biya, kuma ba a saki wani kwamandan ‘yan bindiga ba dangane da aikin ceton daliban.

By
Mohammed Idris Malagi / Nigerian Government

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta musanta zarge-zargen da ke cewa ta biya “makudan kudaden fansa”, tare da sakin wasu kwamandojin ‘yan bindiga, domin samun ‘yancin daliban da aka sace daga makarantar kwana ta St. Mary’s da ke Jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Talata, gwamnatin ta bayyana rahotannin, wadanda aka danganta su da wasu kafafen yada labarai na kasa da kasa a matsayin ƙarya marar tushe da kuma abin da zai iya ɓata martabar jami’an tsaro.

Sanarwar ta ce babu wani kudin fansa da aka biya, kuma ba a saki wani kwamandan ‘yan bindiga ba dangane da aikin ceton daliban.

“Wadannan zarge-zarge ƙarya ne tsantsa, kuma suna tauye ƙwarewa da sadaukarwar da jami’an tsaronmu ke yi a kullum,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta soki rahotannin da cewa sun dogara ne kacokan kan wasu majiyoyi marasa suna da aka bayyana a matsayin “majiyoyin leƙen asiri” ko kuma “wadanda suka san yadda tattaunawar ta gudana,” maimakon bayanan hukuma da aka bayyana a fili.

Ta ce Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da kuma shugabannin Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun fito ƙarara sun musanta batun biyan kudin fansa.

Sanarwar ta kuma bayyana zargin cewa an kai kudin fansa ta jirgin sama mai saukar ungulu ga ‘yan ta’adda, a matsayin kirkirarren labari. DSS ta bayyana wannan zargi a matsayin ƙarya marar tushe.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa an samu nasarar kubutar da daliban ne ta hanyar ƙwarewar leƙen asiri da kuma tsare-tsaren aiki na musamman, ba tare da rasa rai ba.

Ta kara da cewa Nijeriya na fuskantar wani tsararren harkar ta’addanci da aka mayar da ita hanyar neman kudi, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakai bisa doka domin tabbatar da tsaro.

Gwamnatin ta kuma bukaci kafafen yada labarai da su riƙa tantance gaskiya kafin wallafa rahotannin da ka iya ƙarfafa gwiwar masu aikata laifi ko kuma rage ƙwarin gwiwar jami’an tsaro.