26 Nuwamba 2025
Jami’an rundunar da ke sa ido kan Laifuka a Jamhuriyar Nijar ta kama wasu ‘yan kungiyar safarar miyagun kwayoyi a jihar Tahoua a wani aikin samame uku da suka kai jihar.
Jami'ai sun kwato FCFA miliyan 1.7, da kuma dubban kwayoyi na Tramadol, Farin Malam, da Diazepam, tare da wiwi, babura, da wayoyi.
ZA KU SO WAƊANNAN
Hukumomi sun ce aikin ya nuna muhimman matakai da ake dauka wajen dakile laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi a yankin.


















