Hukumomi a Nijar sun kama CFA fiye da miliyan 1.7 da dubban miyagun ƙwayoyi a jihar Tahoua

Jami'ai sun ƙwato FCFA miliyan 1.7, da kuma dubban kwayoyi na Tramadol, Farin Malam, da Diazepam, tare da wiwi, babura, da wayoyi.

By
Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani

Jami’an rundunar da ke sa ido kan Laifuka a Jamhuriyar Nijar ta kama wasu ‘yan kungiyar safarar miyagun kwayoyi a jihar Tahoua a wani aikin samame uku da suka kai jihar.

Jami'ai sun kwato FCFA miliyan 1.7, da kuma dubban kwayoyi na Tramadol, Farin Malam, da Diazepam, tare da wiwi, babura, da wayoyi.

Hukumomi sun ce aikin ya nuna muhimman matakai da ake dauka wajen dakile laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi a yankin.