| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kama surukin tsohon shugaban ƙasar Zambia, Lungu da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar adawa
Sakataren majalisar ministocin Zambia Patrick Kangwa ya ce, an ɗaɗe ana sa ido kan waɗanda aka tsare a tsawon shekaru.
An kama surukin tsohon shugaban ƙasar Zambia, Lungu da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar adawa
Kangwa ya ce ana tuhumar wadanda aka kama kuma za a ba su damar ganawa da iyalansu da lauyoyinsu. / TRT Afrika

‘Yansandan Zambia sun kama mutane 11, ciki har da surukin tsohon shugaban ƙasa Edgar Lungu da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jami’iyyar adawa a wani samame da suka kai a babban birnin ƙasar, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Litinin.

Patrick Mwansa, wanda ke auren 'yar Lungu Tasila, da Brian Mundubile na jam'iyyar National Reconciliation Party for Unity and Progress (NRPUP) suna cikin waɗanda aka tsare bayan samamen da aka kai Lusaka.

Sakataren majalisar ministocin Zambia Patrick Kangwa ya ce, an ɗaɗe ana sa ido kan waɗanda aka tsare a tsawon shekaru.

Kawo yanzu NRPUP ko iyalan Lungu ba su fito fili sun ce komai game da kamen da ‘yansandan ƙasar suka yi ba.

Kangwa ya ce 'yansanda sun samu makamai da harsasai na soja a wurin amma ba su danganta kayayyakin da Patrick Mwansa ko Brian Mundubile ba.

"Aikin ya kai ga ƙwato manyan makamai na soji da kuma kama wasu da ake zargi 'yan ƙungiyar ta'addanci ne da sauran mutanen aka samu a wurin, yayin da wasu suka tsere kuma ba a san inda suke ba," in ji Kangwa.

Kangwa ya ce ana tuhumar wadanda aka kama kuma za a ba su damar ganawa da iyalansu da lauyoyinsu.