| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya na da attajirai 7,200 masu arzikin dala miliyan 1 duk da raguwar kuɗi - Rahoto
A cewar rahoton Nijeriya na da kimanin attajirai 7,200 masu arzikin da ya kai dala miliyan ɗaya, da kuma mutum 20 waɗanda arzikinsu ya haura dala miliyan 100 da kuma hamshaƙan attajirai uku waɗanda kuɗaɗensu suka kai dala biliyan ɗaya.
Nijeriya na da attajirai 7,200 masu arzikin dala miliyan 1 duk da raguwar kuɗi - Rahoto
Dala

Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta a matsayin ƙasa ta huɗu mafi yawan attajirai masu arzikin miliyoyin daloli a Afirka, duk da cewa ta fuskanci ɗaya daga cikin mafi girman raguwar yawan masu hannu da shuni a nahiyar cikin shekaru goma da suka gabata.

A cewar Rahoton Arzikin Afirka na 2025 da Henley & Partners suka fitar tare da haɗin gwiwar New World Wealth, Nijeriya na da kimanin attajirai 7,200 masu arzikin da ya kai dala miliyan ɗaya, da kuma mutum 20 waɗanda arzikinsu ya haura dala miliyan 100 da kuma hamshaƙan attajirai uku waɗanda kuɗaɗensu suka kai dala biliyan ɗaya.

Sai dai rahoton ya nuna cewa wannan adadi na nuni da raguwar kashi 47 cikin ɗari na yawan attajiran Nijeriya tun daga shekarar 2015.

Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a jerin ƙasashen, inda take da attajirai 41,100 masu arzikin da ya kai dala miliyan ɗaya, sai mutum 112 masu arzikin da ya haura dala miliyan 100 sai kuma hamshaƙan attajirai takwas da arziƙinsu ya kai dala biliyan ɗaya.

Masar ce ta biyu da attajirai 14,800 masu arzikin da ya kai dala miliyan ɗaya, sai mutum 49 da arziƙinsu ya kai dala miliyan 100 sai mutum bakwai da arziƙinsu ya kai biliyan ɗaya.

Maroko ce ta zo ta uku da attajirai 7,500 masu arzikin dala miliyan, sai mutum 35 da arziƙinsu ya kai dala miliyan 100 sai hamshaƙan attajirai huɗu da arziƙinsu ya kai dala biliyan  daya, inda ta ɗan fi Nijeriya da kaɗan.

Kenya ce ta cika jerin ƙasashe biyar na farko da attajirai 6,800 masu arzikin da ya kai dala miliyan daya, amma ba ta da ko hamshaƙin attajiri guda.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ba a haɗa wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Tunisiya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), saboda rashin isassun sahihan bayanai.

Mauritius ce ta shida da attajirai 4,800 masu arzikin dala miliyan ɗaya, sai Aljeriya (2,700), Ghana (2,600), Namibiya (2,500) da Habasha (2,400), waɗanda suka cika jerin ƙasashe goma na farko.

Daga cikin ƙasashen da rahoton ya bincika, Seychelles ce ke da mafi ƙarancin adadin attajirai mazauna ƙasar, inda take da attajirai 500 masu arzikin da ya kai dala miliyan daya, hamshaƙin attajiri guda da kuɗinsa ya kai dala biliyan ɗaya da kuma mutum shida waɗanda kuɗaɗensu ya kai dala miliyan 100 shida.