Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Festus Keyamo, ya bayyana a ranar Laraba cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da tsarin yafe wa kamfanonin jiragen saman ƙasar wani ɓangare na basussukan da suke bin hukumomin sufurin jiragen sama.
Wannan mataki ya biyo bayan nasarar tattaunawar da aka yi bayan kamfanonin sun yi barazanar dakatar da aiki saboda tsadar man jirgi da ta ɗurkusar da su.
Kungiyar Masu Kamfanonin Jiragen Sama na Nijeriya (AON) ta yi barazanar dakatar da dukkan zirga-zirgar jirage daga ranar 20 ga watan Afrilu, muddin ba a rage farashin man jirgi ba.
A wata wasiƙa da aka rubuta ranar 14 ga watan Afrilun shekarra 2026 kuma aka aika ga shugaban ƙungiyar manyan dillalan makamashi ta Nijeriya (MEMAN), Mista Clement Isong, AON ta ce farashin man jirgi ya tashi daga ₦900 kan ko wace lita a ranar 28 ga watan Fabrairu zuwa ₦3,300 kan ko wace lita a yanzu — ƙarin fiye da kashi 300 a cikin makonni kaɗan.
Keyamo ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya buƙaci a miƙa masa buƙatar hakan a hukumance cikin gaggawa, inda shi da kansa zai tantance adadin kason da za a yafe daga cikin bashin.
Haka kuma, gwamnati za ta kafa wani kwamiti da zai duba batun haraji da sauran kuɗaɗen da ake karɓa a kan tikitin jiragen saman gida, domin bayar da shawarar rage su don saukaka wa kamfanonin jiragen da ma fasinjoji.
Sakatariyar ma’aikatar man fetur, Patience Oyekunle, ta bayyana bayan kammala tattaunawar ranar Laraba cewa, dillalan man fetur za su zauna da jami’an gwamnati a ranar Alhamis don kokarin warware takaddamar da ake yi kan farashin man jirgin cikin hanzari.
Tsadar man jirgin da aka samu a duniya sakamakon yakin Iran ya girgiza masana’antun sufurin jiragen sama na duniya, wanda hakan ya tilasta wa kamfanoni kara kudin tikiti na zuwa-da-dawowa, takaita shirye-shiryen bunkasa ayyukansu, da kuma sake duba hasashensu na gaba.














