Ghana ta ƙaddamar da bincike a faɗin ƙasar kan samun ɓurɓushin roba a cikin soyayyar plantain

Hukumar mai sa ido ta ce tana aiki da hukumomin cikin al'ummomin da hukumar 'yansandan Ghana domin sa ido kan masu sayarwa.

By
An samu mutuwar mutane ta gubar abinci a baya kuma an alaƙanta shi da gurɓataccan abincin kan layi / Others

Ghana ta ƙaddamar da bincike kan zargin cewa an gano ɓurɓushin roba a cikin soyayyar busasshiyar plantain na sayarwa a faɗin ƙasar.

Hukumar da ke kula da abinci da magunguna a ƙasar (FDA) ta fara sa ido kan kasuwa da kuma gwada plantain ɗin a ɗakin gwaje-gwaje a faɗin ƙasar bayan da wani bidiyo mai yawo a shafukan sada zumunta ya nuna masu suyar suna narka leda cikin mai mai zafi a lokacin suyarda nufin ƙara daskarar da plantain din da kuma daɗewarta a kanti, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito.

Hukumar FDA ta bayyana a wata sanarwa cewa an ƙaddamar da binciken ne domin tabbatar da sahihancin ikirarin da kuma kare masu cin plantain din.

“Narka roba da gangan a cikin man suya gurɓata abinci da sinadari ne kai-tsaye, lamarin da zai sa ya kasance mara kyau ga cin ɗan’adam,” in ji hukumar.

Shigar sinadarai

Hukumar ta FDA ta yi gargaɗin cewa saka kayayyaki na roba cikin mai na matuƙar barazana ga lafiyar al’umma da “ƙara yawan ƙananan robobi da ke shiga cikin abincin,” in ji hukumar.

Hukumar mai sa ido ta ce tana aiki da hukumomin cikin al’ummomi da kuma hukumar ‘yan sandan Ghana domin sa ido kan masu sayar da plantain din da ake zargi da yin abinci da abubuwan da ake ganin na da haɗari ga ‘yan’adam tare da shan alwashin fitar da sakamakon gwajin dakunan gwaje-gwajen da zarar an kammala binciken.

A baya dai ana samun guba ta abinci a ƙasar kuma an alaƙanta hakan da gurɓataccen abincin kan layi da rashin tsafta da kuma rashin ɗabbaka matakan kariyar abinci yadda ya kamata.

A shekarar 2022 hukumar FDA ta rufe wani kantin sayar da abincin tafi da gidanka bayan an yi ta samun gubar abinci da ake alaƙantawa da shi.