Nijeriya da Amurka sun kaddamar da sabbin cibiyoyin aikin tsaro da nufin karfafa haɗin gwiwar tsaro, duk da fargabar da ake da shi game da karuwar hare-haren 'yanta'adda a sassan ƙasar.
A sanarwar da rundunar sojin ta fitar, ta ce an kaddamar da kungiyoyin aikin fasaha na cibiyoyin tsaro (DITWGs) a karkashin taswirar haɗin gwiwar tsaro ta 2026 don "ƙarfafa kokarin hadin gwiwa don magance ayyukan ta'addanci, rashin tsaro da rashin zaman lafiya a yankin."
Sanarwar ta ambato shugaban tawagar Amurka, Cate Dave, yana cewa shirin zai zurfafa tsare-tsare na tsawon lokaci tare da karfafa ayyukan cibiyoyin.
"Shirin zai goyi bayan tsare-tsare na dabaru wadanda za su mayar da hankali da nufin ƙarfafa ayyukan cibiyoyi da kuma hana 'yanta'adda samun mafaka," in ji Dave, yana mai cewa akwai alaka mai karfi tsakanin ci gaban cibiyoyin da ayyukan yaki da ta'addanci.
Kazalika sanarwar ta ambaci shugaban tawagar Nijeriya, Francis Edosa, wanda ya yi nuni kan muhimmancin magance barazanar da ke tasowa.
"Abubuwan da aka fi mayar da hankali akai sun hada da tallafi don karfafa ayyukan yaki na rundunar sojin Nijeriya da kuma kara haɓaka matakan maida martaninta don dawo da zaman lafiya da daidaito mai dorewa a fadin Nijeriya," in ji Edosa.
A cewar sanarwar, ƙasashen biyu sun jaddada bukatar "samar da sakamako mai amfani, daukar nauyi da kuma haɗin gwiwa mai dorewa" don inganta zaman lafiya a ƙasa da kuma yanki.
Tallafin Amurka
Shirin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke fadada tallafin sojojinta ga Nijeriya, ciki har da rahoton tura sojojin Amurka akalla 200 da jiragen sama marasa matuka na MQ-9 da ke aiki daga jihar Bauchi.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Nijeriya Samaila Uba ya ce a baya an tsarin tura sojojin, wanda aka fara a watan Fabrairu, don samar da tallafin tattara bayanai da horo maimakon shiga yakin kai tsaye.
Jami'ai daga ƙasashen biyu sun bayyana cewa ana amfani da jiragen marasa matukan ne kawai don ayyukan leken asiri, sa ido da bincike, inda ma'aikatan Amurka ke aiki a matsayin masu ba da shawara maimakon shiga ayyukan tsaron kai tsaye.
Ƙarin hasken ya biyo bayan damuwar da jama’a suka nuna kan cewa an shigo da sojojin wajen cikin harkokin tsaron cikin gida na Nijeriya.
Duk da ƙarin haɗin gwiwa, Nijeriya na ci gaba da fuskantar mummunan yanayin tsaro. inda ƙungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai kamar Boko Haram da Daesh suke kara kai hare-hare kan sansanonin sojoji da al'ummomin fararen hula, musamman a Arewa maso Gabasin ƙasar.













