Majalisar Dokokin Amurka ta yi gargaḍi kan 'babbar barazanar tsaro' kafin Gasar Kofin Duniya a kasar
Ranar 11 ga Yuni ne za a fara gasar Kofin Duniya ta FIFA a ƙasashen Amurka, Mexico, da Canada.
‘Yan majalisar dokokin Amurka da ke wakiltar biranen da za su karɓi baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA sun ba da bahasi gaban kwamitin majalisa, inda suka bayyana damuwarsu game da matsalolin tsaro da ka iya zama 'masifa' yayin da taron ke ƙaratowa.
A wani taron sauraron ra’ayin jama’a da Kwamitin Tsaron Cikin Gida na Majalisar Wakilai ya shirya, shaidu sun nuna manyan dalilai biyu da suka sa shirye‑shiryen tsaro suka yi jinkiri, duk da cewa saura kusan kwanaki 100 kafin fara gasar.
Sun yi nuni da dakatar da kuɗaɗen asusun FEMA da aka ware don tsaron Gasar Kofin Duniya da kuma rashin haɗin-kai tsakanin hukumomin yankuna da gwamnatin tarayya.
Yayin da gwamnatin tarayya ke cikin dakatar da ayyuka a halin yanzu, FEMA ta sanar ranar Lahadi cewa za ta rage ayyukanta zuwa 'ma'aunin mafi ƙaranci, irin na ceton-rai'. Hakan na nufin an dakatar da duk kudaden da ba su dace da wannan matsayi ba, ciki har da kusan dala miliyan 900 da aka ware wa biranen da za su zama masaukin gasar.
A matsayin wani ɓangare na Dokar One Big Beautiful Bill, FEMA a watan Nuwamba ta ƙaddamar da Shirin Tallafin Kofin Duniya na FIFA, wanda ya ba da dala miliyan 625 ga birane masu masauki don “aiwatar da manyan ayyukan tsaro da ake buƙata don kare 'yan wasa, ma'aikata, masu halarta, wurare, da manyan ababen more rayuwa a faɗin birane masu masaukin, suna ƙarfafa kariyarsa daga yiwuwar harin 'yan ta'adda'.”
Jiragen sintiri
A watan Disamba, hukumar ta bayar da ƙarin dala miliyan 250 ga jihohi 11 masu masauki, tana taimaka musu 'ƙarfafa iyawarsu ta ganowa, tantancewa, bin diddigi, ko rage tasirin tsarin jiragen sama marasa matuƙi.”
“Ina jin da mun yi wannan tattaunawar shekaru biyu da suka wuce, za mu kasance cikin yanayin da ya fi kyau,: in ji Mike Sena, shugaban National Fusion Center Association, a lokacin ba da bahasin, kafin ya ƙara da cewa, “amma yau, yayin da muke kusantar wasannin nan, ba mu kusa kaiwa ikon da muke buƙata ba.”
Ray Martinez, babban jami'in aiwatarwa na Kwamitin Masauki na Gasar Kofin Duniya a Miami, inda ya fayyace buƙatunsa da damuwarsa.
'Muna da kwanaki 107 kafin gasar ta fara, amma mafi muhimmanci, muna da kusan kwanaki 70 kafin fara gina Fan Fest. Idan masu shiryawa ba su samu dala miliyan 70 da suka nema kafin ƙarshen Maris ba, za su fara soke abubuwan, za su fara da Fan Fest.
'Wannan yanke shawara dole a yi. Ba tare da samun wannan kuɗin ba, zai iya zama abin bala’i ga shirin da tsare-tsarenmu.'
Damuwar tsaro
Jami'ai a Foxboro sun yi nuni da yiwuwar janye karɓar baƙuncin wasanni bakwai da aka tsara a Gillette Stadium, idan ba a samu kuɗaɗen ba.
Mataimakin Shugaban 'Yan Sanda na Kansas City, Joseph Mabin ya ce sashen sa a halin yanzu ba shi da isassun ma'aikata don kula duk buƙatun tsaron birnin, kuma ya yi kiran a samar da kuɗi don bai wa birnin damar ɗaukar ƙarin ma'aikata.
Gasar Kofin Duniya, wadda Amurka, Mexico, da Canada ke ɗaukar baƙunci, za ta fara a hukumance a ranar 11 ga Yuni, inda Mexico za ta kara da Afirka ta Kudu a Mexico City, sannan Koriya ta Kudu za ta buga wasa da abokin hamayya da za a tantance a kusa da Guadalajara. Wasan farko da za a buga a Amurka zai zo a ranar 12 ga Yuni, inda Amurka za ta buga da Paraguay a Los Angeles.
Birane 11 a cikin Amurka da za su karɓi baƙuncin su ne Atlanta, Boston, Dallas, Houston, Kansas City, Los Angeles, Miami, New York/New Jersey, Philadelphia, San Francisco Bay Area, da Seattle.