Rikicin PDP: Ɓangaren Wike ya yi watsi da kora yayin da jihohi huɗu ke ƙalubalantar Makinde

Fiye da wakilai 3,000 ne suka taru a birnin na Ibadan ranar Asabar domin zaɓar sabbin shugabannin babbar jam’iyyar adawa duk da hukunce-hukuncen kotu da ke karo da juna.

By
Tun shekarar 2025 rabon jam'iyyar PDP da mulkin Nijeriya

Ɓangaren jam’iiyar adawa ta PDP mai biyayya ga Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi watsi da korar da aka yi wa jiga-jigan jam’iyyar ranar Asabar a wani taron jam’iyyar da aka yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Wannan na faruwa ne yayin da rassan jam’iyyar na jihohi huɗu suka yi watsi da sakamakon taron jam’iyyar, abin da manazarta ke gani a matsayin tawaye ga ƙoƙarin Gwamna Seyi Makinde na yin iko a kan jam’iyyar.

Fiye da wakilai 3,000 ne suka taru a birnin na Ibadan ranar Asabar domin zaɓar sabbin shugabannin babbar jam’iyyar adawa duk da hukunce-hukuncen kotu da ke karo da juna.

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta ba da umarni ranar Jumma’a cewa PDP ta dakatar taronta na ƙasa tare da hana hukumar zaɓe INEC sa ido a taron.

Da yake gabatar da hukunci kan ƙarar da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya shigar, Maishari’a Peter Lifu ya hana hukumar INEC sa ido ko kuma amincewa da taron jam’iyyar ba tare da jam’iyyar ta amince da mai gabatar da ƙarar a matsayin ɗan takara ba

Mai Shari’a Lifu ya yanke hukuncin cewa hujjoji da ke gaban kotun sun tabbatar da cewa an hana Lamido damar sayen takardar takarar a shugaban jam’iyyar ne cikin rashin adalci, wani matakin da ya saɓa wa tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokokinta na cikin gida.

Kotun ta kuma bayyana cewa dole PDP ta samar da damarmaki wa mambobinta domin su iya neman muƙamai da suka dace da burikansu na siyasa

Saboda haka Mai Sharia Lifu ya ba da umarnin cewa a dakatar da taron da aka shirya yi domin a bai wa Lamido damar sayen takardar takara ya tara magoya baya da kuma yin gangamin zaɓe.

Sai dai kuma wani hukunci da ya ci karo da wannan ya fito da Babbar Kotun jihar Oyo da ke zaune a Ibadan wadda ta ba da izinin a ci gaba da taron jam’iyyar.

Mai Shari’a Ladiran Akintola ya ba da izinin yin taron a lokacin da yake yanke hukunci kan wata ƙarar da wani mambar jam’iyyar PDP na jihar Oyo, Mista Folahan Adelabi, ya shigar inda ya nemi kotun ya bai wa INEC umarnin kasancewa a taron jam’iyyar.

Hukunce-hukuncen Kotu masu karo da juna sun raba jam’iyyar gida biyu inda inda ɗaya ke biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, yayin da ɗaya ke samun goyon bayan gwamnonin PDP da sauran rassan jam’iiya.

A lokacin taron jam’iyyar ta amince da kudirin tsohon shugaban kwamitin amittatun jam’iyyar, Bode George, na korar Nyesom Wike da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da tsohon mataimakin shugaban  jam’iyyar a kudu maso kudancin ƙasar, Cif Dan Orbih da sauransu.

Sai dai kuma ɗaya daga cikin shugabannin PDP da aka kora a taron, Abdulrahman Mohammed ya bayyana lamarin a matsayin abin dariya, yana mai shan alwashin ci gaba da aikinsa a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar.

An naɗa Mohammed a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar ne bayan ɓangare mai biyayya ga Wike ya dakatar da tsohon shugaban jam’iyyar, Umar Damagum da ma dukkan mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar gabaɗaya.

Jaridar Punch ta ambato Mohammed yana cewa shi ba zai bar shugabancin jam’iyyar ba yana mai jaddada cewa ba a yi taron jam’iyyar a Ibadan ba.

“Abin da ya faru a Ibadan ba taron jam’iyya ba ne. An yi shi ne saɓanin sahihin umarnin kotu. Ka da ‘yan Nijeriya su tayar da hankalinsu saboda PDP tana kan hanyarta ta ba su shugabanci na-gari,” in ji shi.