Victor Osimhen, Zaidu Sanusi da Muhammad Usman na cikin ‘yan Super Eagles da za su je AFCON 2025
Fitaccen ɗanwasan Super Eagles, Victor Osimhen, da ke murza leda a Galatasaray ta Turkiyya da Ademola Lookman da Akor Adams da Moses Simon na cikin jerin ‘yanwasan da za su fafata a gasar AFCON 2025 a ƙasar Maroko.
Kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 28 da za su wakilci tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya a gasar cin kofin Afirka ta AFCON 2025 da za a fara a ƙasar Maroko a watan Disamba.
A cikin jerin ‘yan wasan da kocin ya fitar ranar Alhamis, akwai Zaidu Sanusi wanda yake buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Porto da ke ƙasar Portugal.
Kazalika akwai Usman Muhammad Edu, ɗan wasan tsakiya da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ironi Tiberias ta Isra’ila.
Akwai kuma Salim Fago Lawal, wani ɗanwasan gaba da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta NK Instra 1961 ta ƙasar Croatia.
Fitaccen ɗanwasan Super Eagles, Victor Osimhen, da ke murza leda a Galatasaray da Ademola Lookman, mai wasa a Atalanta na Italiya da Akor Adams na Sevilla da Moses Simon na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris na cikin jerin ‘yanwasan da za su wakilci Nijeriya a gasar.
Har wa yau akwai Kelvin Bassey da ke taka leda a Fulham da Semi Ajayi na Hull City da Bright Osayi-Samuel da ke wasa a Birmingham City da Bruno Onyemaechi da ke taka leda a Girka.
Kazalika a cikin jerin ‘yanwasan akwai Wilfred Ndidi da ke wasa a Besiktas da Frank Onyeka da ke Brentford da Fisayo Dele-Bashiru da ke wasa a Lazio da Alex Iwobi da ke wasa a Fulham.
Akwai kuma Stanley Nwabali wanda ke kama gola a Chippa United ta Afirka Ta Kudu da Francis Ozoho da ke kama gola a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Omonia da ke Cyprus.
Ranar 21 ga watan Disamba ne dai za a fara gasar cin kofin Afirka ta AFCON 2025 inda ƙasashe 24 za su fafata domin neman cin kofin Afirka.