| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Wani jirgin sojin Amurka ya faɗi a yammacin Iraƙi
Cibiyar tsaro ta Amurka ta tabbatar da cewa wani jirgi samfurin KC-135 ya faɗi a Iraƙi, yayin da wani ya sauƙa lafiya.
Wani jirgin sojin Amurka ya faɗi a yammacin Iraƙi
Wani jirgin Amurka samfurin KC-135 ya faɗi a yammacin Iraƙi / Reuters / Reuters
13 Maris 2026

Wani jirgin Amurka samfurin KC-135 ya faɗi a yammacin Iraƙi yayin da wani ya sauƙa lafiya, in ji rundunar sojin Amurka.

"Ɗaya daga cikin jiragen ya faɗi a yammacin Iraƙi, kuma ɗayan ya sauƙa lafiya. Ba abokan gaba ne suka harbo jirgin ba," in ji cibiyar tsaron ta Amurka (CENTCOM), wadda ke da alhakin kula da dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya, in ji sanarwar.

Jirgin samfurin KC-135 shi ne aƙalla jirgin Amurka na huɗu da aka rasa yaƙin Iran, bayan an harbo jirage samfurin F-15 uku da a sararin samaniyar Kuwait.

Masu AlakaTRT Afrika - Ministan harkokin wajen Iran ya kawar da yiwuwar tattaunawa da Amurka

Jiragen KC-135s, waɗanda suka shafe fiye da shekaru 60 suna aiki, sukan ɗauki ma’aikata uku ne: matuƙan jirgi biyu da kuma wanda yake sarrafa bututun da ake amfani da shi wajen bai wa sauran jirage mai, in ji rundunar sojin saman Amurka.

Amma wasu ayyukan KC-135 na buƙatar na’urar gane-mini-hanya, kuma jirgin zai iya ɗaukar fasinjoji 37, kamar yadda wata takardar bayanai ta rundunar sojin sama ta bayyana.

Da farkon yaƙin, wanda aka fara ranar 28 ga watan Fabrairu, dakarun Kuwait sun kakkaɓo jirgagen yaƙin Amurka samfurin F-15E, amma dukkan jami’an cikin jiragen shida sun iya fitar da kawunansu, in ji CENTCOM.

Wancan lamarin ya auku ne a lokacin yaƙi, ciki har da "hare-hare daga jirgin saman Iran da makamai masu linzami da jirage mara matuƙa," in ji rundunar ta soji a wancan lokacin.

Rumbun Labarai
Sharuɗɗa 10 na zaman lafiya da Amurka ta amince da su a yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
Mazauna Tehran sun fada halin rashin tabbas bayan barazanar Trump ta baya bayan nan
Abubuwan da ya kamata mu sani game da daftarin yarjejeniyar Amurka da Iran
Masar ta haɗa kai da Turkiyya da Pakistan don shiga tsakanin Iran da Amurka – Kafafen  Yaɗa Labarai
Amurka da Iran na duba yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 45: Rahoto
Amurka ta ceto direban jirgin F-15 na biyu da ake nema a Iran — Trump
Tururin nukiliya zai jawo asarar rayuka a manyan biranen ƙasashen Gulf ba Tehran ba: Araghchi
Farashin kayan abinci, man fetur da takin zamani ya ƙaru saboda yaƙin Gabas ta Tsakiya: MDD
Yadda yakin Gabas ta Tsakiya zai shafi ƙasashen Afirka a gajeren lokaci, in ji wani rahoto
Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35
Makamai masu linzami na Iran na jarraba ƙarfin garkuwar makamai masu linzami a sararin samaniya
Iran ta ce Mashigar Teku ta Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe ga maƙiya
Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra’ila bayan Trump ya yi iƙirarin daƙile ƙarfin sojinta
Isra’ila ce ummul aba'isin haramtaccen yaƙi da Iran: In ji Erdogan na Turkiyya
Kalin ya karɓi baƙuncin tawagar Hamas don tattauna shirin zaman lafiya na Gaza
Trump ya ce Amurka za ta bar Iran cikin makonni 2 zuwa 3
Iran ta ce lokaci ya yi da Saudiyya za ta kori sojojin Amurka daga yankinta
Yadda yaƙin Iran zai iya rikita kasuwancin duniya ta Mashigar Teku ta Bab al Mandeb
Ubangiji ba ya karɓar addu'ar waɗanda suke ƙaddamar da yaƙi - Fafaroma
Trump na son ƙwace man Iran, ya sa ido a Tsibirin Kharg yayin da dakarun Amurka ke son shiga— rahoto