Kundin Guinness World ya dakatar da karbar duk wata buƙata daga Isra’ila: Rahoto

Kafafen watsa labarai na Isra’ila Guinness ya dakata da karbar duk wata bukata daga Isra’ila ta shiga kundin bayan wani yunkuri na neman amince wa da kyautar koda.

By
Guinness bai ce komai ba game da ikirarin. [FILE]. / AA

Kundin Guinness World ya yanke shawarar dakatar da duk wata mu'amala da Isra'ila, inda ya toshe duk wata dama ta mika masa wani bayani, ciki har da bukatar tabbatar da bayanan bayar da gudunmawar ƙoda a Isra'ila, a cewar wani rahoto na kafofin watsa labarai na cikin gidan kasar.

Channel 12 ya rawaito a ranar Laraba cewa wata kungiyar sa kai mai suna "Kyautar Rai," wacce ke tallata bayar da gudunmawar koda, ta tuntubi Guinness don yin rijistar wani muhimmin cigaba da ya shafi masu bayar da gudunmawar Isra'ila 2,000 wadanda suka ceci rayuka ta hanyar bayar da gudunmawar sassan jiki.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa an "ki amincewa da bukatar ne saboda dalilai na siyasa."

Kungiyar ta biya kudade kuma ta shirya wani biki a Yammacin Urushalima don daukar hotunan dukkan masu bayar da gudunmawar su 2,000 a tare don a saka su cikin kundin Guinness, amma ta sami sakon email daga Guinness cewa: "Ba ma karbar takardun neman shiga kundin daga Isra'ila a halin yanzu."

Tun daga lokacin kungiyar ta yi kokarin fahimtar dalilin da kuma ko za a iya sauya shawarar, amma ba ta sami amsa ba, in ji kafar watsa labaran.

Rabbi Rachel Haber, wanda ke jagorantar kungiyar, ya kira kin amincewa da Guinness din ya yi da wannan nasara a matsayin "abin da ba za a yarda da shi ba."

Guinness bai ce komai kan wannan ikirarin ba.

Rahoton ya zo ne yayin da Isra'ila ke fuskantar wariya mai tsanani da ke da alaƙa da kisan kare dangi na shekaru biyu da ta yi a Gaza, wanda ya haifar da ware ta a harkokin ilimi, al'adu, siyasa da wasanni.

Tun daga watan Oktoban 2023, sojojin Isra'ila sun kashe mutane sama da 70,000 a Gaza, galibi mata da yara, tare da raunata wasu sama da 171,000 a munanan hare-haren da suka jefa yankin cikin mawuyacin hali.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba, amma sojojin Isra'ila sun saba yarjejeniyar tsagaita wuta tun daga lokacin da aka fara aiki da ita.