| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Erdogan zai kai ziyara Saudiyya don tattaunawa da Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan
Ziyarar ta shugaban Turkiyya Erdogan ta zo ne a daidai lokacin da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ke ziyara a Saudiyya don tattaunawa kan dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma ci-gaban yankin.
Erdogan zai kai ziyara Saudiyya don tattaunawa da Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan
Ana sa ran Erdogan zai gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya da kuma Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a Saudiyya ranar Jumma'a, in ji Burhanettin Duran, shugaban hukumar sadarwa ta Turkiyya.

A yayin ziyarar, ana sa ran Erdogan zai gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya kana Firaminista Mohammed bin Salman da kuma Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, kamar yadda Duran ya bayyana a ranar Alhamis a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta ta NSosyal ta Turkiyya.

A ɓangare guda, Sharif ya isa Saudiyya don ziyarar kwanaki uku wadda ta mayar da hankali kan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu da ci-gaban yankin.

Kamfanin dillancin labarai na SPA na Saudiyya ya ce Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz kana mataimakin gwamnan yankin Makkah, ne ya tarbi Sharif a filin jirgin saman Sarki Abdulaziz da ke Jeddah.

Kazalika a cewar, kamfanin dillacin labarai na Pakistan (APP), Sharif ya samu rakiyar Field Marshal da Babban Hafsan Sojan Kasa Asim Munir kana Mataimakin Firaminista da kuma Ministan Harkokin Waje Ishaq Dar, da sauran manyan jami'ai.

An shirya Sharif zai yi tattaunawa da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman kan hanyoyin karfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, da kuma ci gaban yankin da ma duniya baƙi daya, in ji APP.

Saudiyya da Pakistan suna da kyakkyawar alaƙa ta tsaro a ƙarƙashin yarjejeniyar tsaro da aka sanya wa hannu a yayin rikicin yankin.

Ziyarar ta zo ne yayin da Islamabad ke ci gaba da ƙoƙarin shiga tsakani Washington da Tehran.

A watan Yuni, Qatar ta haɗa kai da Pakistan wajen shiga tsakanin Amurka da Iran, wanda ya kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a ranar 18 ga Yuni da kuma fara tattaunawa don cim ma yarjejeniya ta ƙarshe.

Daga baya tattaunawar ta tsaya cak kan rashin jituwa da ta shafi tsaron teku da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz, ko da yake jami'ai daga Iran da Oman da kuma Amurka sun nuna alamun ci gaba da warware sauran batutuwan.