An fara Baje-Kolin Kayan Tsaro da Sufurin Sararin Samaniya na Turkiyya SAHA 2026 inda aka bude kofa ga maziyarta a Cibiyar Expo ta Istanbul a ranar Talata, kuma kamfanoni 1,700 ciki har da 263 na kasa da kasa da sama da kwararru 30,000 daga kasashe fiye da 120 ke halarta.
Ƙungiyar kamfanonin tsaro mafi girma a Turai da Turkiyya, SAHA Istanbul ne ke shirya baje-kolin. Za a ci gaba da baje-kolin har nan da 9 ga Mayu.
Ana baje-kolin ne a waje mai girman murabba’in mita 400,000. SAHA ta ware wajen da ba a rufe ba mai girman murabba’in mita 20,000 don baje kayan tsaron, wanda hakan ya sanya baje-kolin kayan tsaro mafi girma zuwa yau.
Fiye da kamfanoni 1,700 ciki har da 263 na kasa da kasa da sama da kwararru 30,000 daga kasashe fiye da 120 ke halarta.
Jimillar sabbin kayan tsaro 203 ne za a gabatar, za a sanya hannu kan yarjeniyoyi 164 a yayin SAHA 2026. Taron na da manufar samar da fitar da kayayyakin tsaro sama da na dala biliyan 6.2 da aka samu a baje-kolin 2024.
Halartar baje-kolin daga Amurka da Turai da Canada ya zama na musamman, inda kamfanoni da wakilansu ke halarta daga nahiyoyi hudu.
Kayayyaki da dama za su hadu da kasuwarsu a karon farko a wajen SAHA 2026.
Za a baje-kolin wata motar yaki ta ruwa marar matuki a wajen.
Kamfanonin tsaro na Turkiyya na baje-kolin sabbin fasahohi
A a baje-kolin sabbin fasahohi a karon farko a wajen taron na SAHA 2026.
Kamfanin samar da jirage marasa matuki na Turkiyya, Baykar zai gabatar da Mizrak, wanda ta yi fice da fasahar Kirkirarriyar Basira da ikon harbi zuwa nisan kilomita 1,000.
A wajen SAHA 2026 za kuma a baje-kolin jiragen yaki marasa matuka na K2 Kamikaze da Sivrisinek.
Wani babban kamfanin kayan tsaro na Turkiyya Aselsan ma zai gabatar da sabbin kayayyaki biyar da wasu shida da aka kara wa karfi.
Haka zalika, kayan tsaron da Roketsan da FNSS suka samar da hadin gwiwa za su bayyana a SAHA 2026.
Sannan kuma Roketsan, zai gabatar da kayansa mafi gitman fasaha, inda STM kuma zai gabatar da kayan tsaron dama sa na ruwa sa aka samar don yakin zamanin yau.
Baje-kolin na karbar bakuncin jami’ai na hukumomi sama da 140, sama da wakilan gwamnatoci 800 da kuma wakilan sayar da kayayyaki sama da 200.
Za a ci gaba da baje-kolin SAHA 2026 har nan da 9 ga Mayun 2026.













