| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Mbappe ya mayar da martani ga Sanatar Paraguay da ta zagi launin fatarsa
Kylian Mbappe ya kira Sanatar, Madame Celeste Amarilla, da "mutuniyar banza" wadda "ba ta cancanci matsayin" Sanata mai wakiltar al'ummar Paraguay ba.
Mbappe ya mayar da martani ga Sanatar Paraguay da ta zagi launin fatarsa
Kwallon kafa na Kofin Duniya: Paraguay da Faransa / AP

Tauraron ɗanwasan Faransa, Kylian Mbappe, ya mayar da zazzafan martani ga wata Sanatar ƙasar Paraguay, wadda ta yi masa kalaman cin zarafi bayan Faransa ta fitar da ƙasarta daga Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026.

Bayan wasan na ƙarshen makon da ya gabata, Sanata Madame Celeste Amarilla ta zagi launin fatar Mbappe, a shafin X.

Ta kira shi "ɗan Kamaru wanda ke ƙangin mulkin mallaka, mai neman a ce Bafaranshe ne shi…, gardi wanda bai koyi karatu ba”.

Mbappe, wanda shi ne kyaftin ɗin tawagar Faransa, ya kira kalaman Sanatar da na wariyar launin fata, kuma ya ce mata "mutuniyar banza".

Sannan ya kare ‘yan tawagarsa da ma 'yan tawagar Paraguay, waɗanda ya kira da jajirtattun ‘yanwasa masu mutunci da suka wakilci ƙasarsu”.

Ita ma hukumar ƙwallon ƙafa ta Faransa, FFF, ta ce ta ɗauki mataki kan batun, kuma ta sanar da shirin shigar da ƙara kan munanan kalaman matar".

Da ma tun kafin wasa, tsohon golan Paraguay, Jose Luis Chilavert, ya ce tawagar ƙasarsa za ta kara ne da "wata tawaga daga Afirka", kalaman da shugaban FFF ya kira “abin kunya”.