Yadda barazanar da Trump ya yi kan aika sojoji Nijeriya ta tayar da ƙura
Trump ya bayar da umarnin ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, kwana guda bayan da ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Babban labarin da yake ci gaba da daukar hankali a Nijeriya ko ma a ce a duniya, shi ne matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai dauka kan Nijeriyar, inda ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirye-shiryen yiwuwar kai hari kasar, bayan da Trump din ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a kasar.
Trump ya bayar da umarnin ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, kwana guda bayan da ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani ga Amurka bayan ƙasar ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla, inda kuma ta saka Nijeriyar cikin jerin kasashen da ake saka wa ido saboda karancin ‘yanci da walwalar addini.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin-kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ’yan ƙasa daga kowane yanki da addini.
Tinubu ya kara da cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ’yancin yin addini.
Ina batun ya dosa?
Masana harkokin tsaro da diflomasiyya suna ganin gwamnatin Nijeriya ba ta ga ta zama ba. Ya kamata Shugaba Tinubu ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya yi ganawa ta keke-da-keke da Shugaba Trump, inda zai fayyace masa cewa ba gaskiya ba ne batun cewa mabiya addinin Kirista kawai ake kashewa a Nijeriya, kuma ya nuna masa sahihan alkaluman da za su gaskata hakan.
Sannan ya bayyana masa cewa babu wani shiri da gwamnatin kasar take da shi na kisan wasu mabiya addini. Kuma shugaban zai iya buga misali da shi kansa cewa shi Musulmi ne amma matarsa Kirista ce kuma a cikin ’ya’yansa akwai mabiya addinin Kirista, sakamakon haka babu yadda za a yi gwamnatinsa ta zuba ido ana kashe Kiristoci a kasar.
Abu na biyu da ya kamata gwamnatin ta yi shi ne gaggauta nada jakadu na dindindin a ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke kasashen ketare, kamar yadda jigo a jam’iyyar NNPP Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na Facebook.
Masana diflomasiyya na ganin nadin jakadun zai taimaka wajen kare kimar Nijeriya a tsakanin kasashen duniya, kuma zai taimaka wajen daukaka muradun kasar musamman a wannan muhimmin lokaci da ake ciki.
Kazalika, shugaban cibiyar tsaro ta Beacon Consulting a Nijeriya, kuma masani kan al’amuran da suka shafi zamal lafiya, Malam Kabiru Adamu, ya ce akwai bukatar Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Maitama Tuggar ya gana da jakadan Amurka da ke Nijeriya don ya fayyace masa ainihin abubuwan da ke faruwa ta fuskar tarin matsalolin tsaron da kasar ta kwashe shekaru da dama tana fama da su.
Dar Adamu ya shaida wa gidan talabijin na Nijeriya, NTA cewa akwai bukatar Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) da Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA) su yi wani zama na musamman, kuma bayan zaman su fitar da sanarwar hadin-gwiwa kan cewa tabbas ana kashe-kashe a Nijeriya wanda yake rutsawa da Kiristoci da kuma Musulmai. Don haka, babu mabiyan wani addini da za a ce su kadai ne hare-haren da kashe-kashen yake shafa.