Ken Ofori-Atta: Ghana ta buƙaci Amurka ta tisa ƙeyar tsohon ministan kuɗin ƙasar

Gwamnatin Ghana ta miƙa buƙata a hukumance ga Ma’aikatar Shari’a ta Amurka domin a tisa ƙeyar Tsohon Ministan Kuɗi na Ghana Mista Ken Ofori-Atta da kuma babban mataimakinsa Mista Ernest Darko Akore, don su fuskanci tuhuma.

By
Ken Ofori-Atta ya kasance Ministan Kuɗi na Ghana na tsawon shekara bakwai a ƙarƙashin Shugaba Nana Akufo-Addo / Getty

Babban Lauyan Ghana kuma Ministan Shari’a na ƙasar, Dakta Dominic Akurutinga Ayine, ya miƙa buƙata a hukumance ga Ma’aikatar Shari’a ta Amurka domin a tisa ƙeyar Tsohon Ministan Kuɗi na Ghana Mista Ken Ofori-Atta da kuma babban mataimakinsa Mista Ernest Darko Akore, don su fuskanci tuhuma.

Da yake magana a taron manema labarai na bayar da bahasi na gwamnati a Accra, Dakta Ayine ya ce Ofishin Mai Shigar da Ƙara na Musamman ya binciki zargin ayyukan cin hanci da suka shafi tsohon Ministan Kuɗin da abokan aikinsa suka aikata, sannan ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Shari’a a kansu.

Ya ce a ranar 19 ga Nuwamba, ofishinsa ya karɓi buƙata a hukumance daga Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman domin fara matakan tisa ƙeyar Ken Ofori-Atta da Mista Ernest Darko Akore daga Amurka.

Ya bayyana cewa bayan nazari na farko, Sashen Haɗin Kai na Ƙasa da Ƙasa na ofishinsu ya lura cewa akwai wasu sassa na buƙatar batun tasa ƙeyar da suke buƙatar ƙarin bayani da gyara domin su dace da ƙa’idojin doka da na tsari da ake bukata.

Dakta Ayine ya ce sun sanar da Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman waɗannan bayanai ta wata wasika mai kwanan wata 25 ga Nuwamba, tare da neman ƙarin takardu domin tabbatar da cikakken bayani.

Ya ƙara da cewa a ranar 9 ga Disamba, Ofishin Mai Gabatar da Ƙara na Musamman ya bayar da ƙarin takardun da aka nema tare da gyara wasu kurakurai, inda aka kammala da buƙatar tasa ƙeyarsu.

Babban Lauyan Ƙasa ya ce daga bisani, a ranar 10 ga Disamba, ofishinsa ya tura cikakkiyar buƙatar ga Ministan Harkokin Waje domin a isar da ita ga hukumomin da suka dace a Amurka, wato Ma’aikatar Shari’a ta Amurka.

“A wannan mataki, ya rage ga hukumomin Amurka, musamman hukumomin shari’a, su yanke hukunci kan ko akwai isasshen dalili da zai sa a miƙo waɗannan mutane biyu zuwa Ghana domin su fuskanci shari’a,” in ji Dakta Ayine.