| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Jamal Musiala na Bayern Munich ya ce farfaɗiyar sandarewa ce ke damun sa
Da yake jawabi a Instagram, ɗanwasan ɗan asalin Jamus ya ce, "Na san da yawanku kun shiga damuwa. Ina so na kawar da damuwar yau, na yi bayani kan lamarin: An gano ina fama da farfaɗiyar sandarewa ta ɗan lokaci, amma ana iya magance ta.
Jamal Musiala na Bayern Munich ya ce farfaɗiyar sandarewa ce ke damun sa
Shekarun Jamal Musiala 23 a duniya.

Bayan yanke jiki yana faɗuwa a filin wasa har sau biyu cikin kwanaki huɗu, matashin ɗanwasan Bayern Munich, Jamal Musiala ya bayyana cewa yana fama da ciwon farfaɗiya mai sa sandarewa, wadda cuta ce da ake iya warkewa.

Mai shekaru 23, Musiala ya zube a ƙasa mintuna kaɗan bayan ya shiga filin wasa ranar Talata, inda Bayern Munich ta buga wasan sada-zumunta da Heidenheim, lokacin aka sako shi a zagaye na biyu na wasan.

An ga ‘yanwasan duka ƙungiyoyin biyu sun yi masa ƙawanya yayin da yace kwance a filin wasa yana samun kulawar likita, kafin daga bisani a taimaka masa ya fita daga filin.

Gabanin nan, Musiala ya yanke jiki ya faɗi ranar Asabar yayin wani wasan na sada-zumunta da Bayern ta buga da RB Leipzig, inda nan ma aka duba lafiyarsa kafin ya fice daga filin da kansa.

Da yake jawabi a Instagram, ɗanwasan ɗan asalin Jamus ya ce, "Na san da yawanku kun shiga damuwa. Ina so na kawar da damuwar yau, na yi bayani kan lamarin: An gano ina fama da farfaɗiyar sandarewa na ɗan lokaci, amma ana iya magance ta.

Jinyar karaya

"Wannan ciwo na iya haddasa irin abin da aka gani kwanan nan, kamar lokacin wasanmu da Leipzig ko wasanmu da Heidenheim. Na san abin na da bantsaro idan ka gani, amma a wajena, wannan yanayi ne na rayuwata ta kullum”.

Ya kuma ƙara da cewa yana karɓar magani saboda ƙungiyarsa ta Bayern da abokan arziƙi suna tare da shi suna taimaka masa a halin da yake ciki."

Da ake tambayar Daraktan Wasanni na Bayern Munich, Max Eberl bayan wasan Talata kan me ya sa aka saka Musiala a wasa duk da ya faɗi ranar Asabar ɗin da ta gabata, ya ce sun san da lamarin kuma ɗanwasan zai yi bayani.

Ko a bazarar bara ma, Jamal Musiala ya karya ƙafarsa ta hagu a gasar Kofin Duniya na Ƙungiyoyi, lokacin wasan Bayern Munich da Paris Saint-Germain.

Sai a farkon 2026 ne ya dawo buga gasar Bundesliga ta Jamus, sannan ya buga gasar Kofin Duniya tare da tawagar Jamus, inda aka cire su a zagayen ‘yan-32.

Yanzu dai za a jira ganin ko Jamal Musiala zai buga wasan gasar German Supercup, inda zakarun gasar Bundesliga, Bayern za su kece raini da Borussia Dortmund ranar Asabar mai zuwa.