| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Iran ta ce dole Amurka ta ba da biza ga tawagarta ta Kofin Duniya ba tare da la'akari da siyasa ba
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje ya ambata fatan cewa FIFA za ta ɗauki matakan da suke wajaba 'domin kare mutuncin gasar'.
Iran ta ce dole Amurka ta ba da biza ga tawagarta ta Kofin Duniya ba tare da la'akari da siyasa ba
'Yan wasan Iran yayin da suke daukar hoton rukuni kafin wasa da Costa Rica, a Antalya, Turkiyya, 31 ga Maris, 2026 (HOTO NA AJIYA) / Reuters

Ma'aikatar Harkokin Waje ta Iran ta ce Amurka, a matsayinta na mai masaukin Gasar Kofin Duniya ta FIFA, tana da alhakin ba wa tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran biza duk da bambance-bambancen siyasa tsakanin ƙasashen biyu.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje ta Iran, Esmaeil Baghaei, ya faɗa a daren Laraba cewa Tehran na yin 'dukkan ƙoƙarin da zai yiwu' don tabbatar da cewa ba za a samu wata matsala ba ga tawagar ƙasar Iran yayin halartar ta a Gasar Duniya a Amurka.

''Yan wasan mu za su tafi Amurka ne kawai don Gasar Kofin Duniya,' in ji Baghaei, bayan wani wasan atisaye na cikin gida, kamar yadda gidan jaridar Mehr na Iran ya amabato.

Ya ƙara da cewa ƙasa mai masaukin baƙi na da 'bayyananne kuma takamaiman alƙawari da dole ne ta kiyaye,' yana jaddada cewa dole ne a ba wa 'yan tawagar Iran biza 'ba tare da la'akari da batutuwan siyasa ba'.

Baghaei ya kuma bayyana fatan cewa FIFA za ta ɗauki matakan da suka dace 'don kare mutuncinta,' yana mai cewa abubuwan da suka faru kwanan nan da suka shafi tawagar Iran 'ba su dace da tsarin FIFA ba'.

Ya ce Iran za ta yi amfani da 'dukkan damar da take da ita' don sauƙaƙa al'amuran da suka shafi halartar tawagar.

Batun tattaunawa

Da yake nuni da rashin hulɗar diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka, Baghaei ya ce Sashen Muradun Iran a Washington ya shirya sosai don ba da taimakon da ake buƙata.

A lokacin da aka tambaye shi game da tattaunawa, Baghaei ya ƙi yin tsokaci, inda ya ce: 'A yanzu muna mayar da hankali ne kan wasanni.'

Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 za ta gudana ne a ƙasashen Amurka, Canada da Mexico, daga 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yuli.

An shirya Iran za ta buga wasanni biyu a Los Angeles tare da New Zealand ranar 15 ga Yuni, da kuma tare da Belgium ranar 21 ga Yuni, kafin ta fafata da Masar a Seattle ranar 26 ga Yuni.

Amurka da Isra'ila sun kai farmaki kan Iran ranar 28 ga Fabrairu, abin da ya sa Tehran ta kai hare-haren ramawa kan Isra'ila da kadarorin Amurka a yankin Gulf, abin da ya haifar da tarnaƙi a Mashigin Hormuz.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki ran 8 ga Afrilu bayan sulhun Pakistan, amma tattaunawar a Islamabad ba ta samar da wata yarjejeniya mai ɗorewa ba.

Daga bisani, Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara wa’adin tsagaita-wutar ba tare da fayyace iyakarta ba.