Mireille Bondo tana ɗaukar jarkoki guda biyu masu girman lita 20 zuwa fiye da kilomita ɗaya wajen da rijiyar birtsatse take a kowace safiya. Famfon da ke ƙarshen lungunsu ya bushe tsawon shekaru biyu.
"Ya'yana suna buƙatar ruwa don yin wanka su tafi makaranta, kuma ni ma ina buƙatar shi don ƙananan kayan lambu da nake sayarwa," in ji matar mai shekaru 32, 'yar asalin Lukalaba a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, a tattaunawarta da TRT Afrika. "Suna cewa muna da shirin samar da isasshen ruwa a wannan ƙasar. A yanzu, ɗaukar jarkoki a bayana shi ne shirin."
Fiye da kilomita 4,000 daga bangaren gabas, a cikin ɗaya daga cikin matsugunan marasa galihu da ke Nairobi, Duncan Ochieng mai shekaru 17 yana kan layi a wajen bandakin jama'a wanda gidaje sama da hamsin ke amfani da shi. Ƙofofin kowane banɗaki ta karye. Dole mutum ya shaki warin da ke fitowa.
"Kuna zuwa da sauri, kuma kuna fatan ba za ku yi rashin lafiya ba," in ji shi.
Abin da ya fi tsorata matashin ɗan Kenya shi ne ruwan sama. "Lokacin da ambaliyar ruwa ta afku, wannan wuri gaba ɗaya ya zama…. bayan gida," in ji shi. "A bara, ƙanwata ta yi rashin lafiya sosai saboda ruwan. Likitan da ke asibitin ya ce kwalara ce."
A duk faɗin biranen Afirka masu cike da jama'a, miliyoyin mutane suna maimaita irin wannan tsari kowace safiya - ɗebo ruwa, guje wa gurɓataccen ruwa, da kuma kula da lafiya da sauran hatsarin da kayayyakin more rayuwa na jama'a ya kamata su iya ragewa.
Wani sabon bincike na duniya ya bayyana matsalar da ke tattare da waɗannan biranen da manufofi da ke kan takarda kawai wadanda tsarin da ba ya aiki a zahiri ke tafiyar da su.
Matsalar ta fi karfin ta shimfida bututu
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan Binciken Tsabtace Ruwa da Ruwan Sha na GLAAS na 2025, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da UNICEF suka tattara, ya samo asali ne daga bayanan da aka tattara a ƙasashe 105.
Babban abin da aka gano shi ne rashin jituwa tsakanin abin da gwamnatoci suka yi alkawari da abin da ake yi wa 'yan ƙasa.
Ƙasa da kashi 13% na ƙasashe suna da albarkatun kuɗi da na ɗan adam don aiwatar da shirye-shiryensu na ruwa, tsafta da tabbatar da inganci. A cikin kashi 64% na ƙasashe, nauyin da gwamnati ke ɗauka a bangaren na haifar da maimaituwa da ruɗani maimakon daidaita al’amura..
Gibin kuɗi tsakanin buƙatun da ake da su da kayayyakin da ake da su ya kai kashi 46%.
"Da yake ƙasa da shekaru biyar suka rage don cim ma burinmu na 2030 (ruwan sha mai lafiya da araha ga duniya da kuma samun damar tsafta), muna cikin mawuyacin lokaci," in ji Dr Alvaro Lario, shugaban UN-Water.
Ga biranen Afirka, sakamakon ya zama a bayyane karara. Akwai wata hanyar samar da ruwa, amma matsugunan marasa galihu ba sa samun ruan mai tsafta. Za a iya samar da tsarin tsaftar ƙasa, amma kasafin kuɗin birane ba zai iya kaiwa ga ayyukan kula da magudanar ruwa da masai ba..
Jimillar mutane biliyan 2.1 a duniya na rayuwa ba tare da ruwan sha mai tsafta ba, inwa wasu biliyan 3.4 kuma ba sa samun damar tsaftataccen muhallai. Biranen Afirka na da kaso mai yawa na wannan matsalar ta lafiyar jama'a.
Ta kai ga ruwan da ke shiga tsarin yana ɓuɓɓuga. A matsakaici, kashi 39% ana rarraba su a matsayin ruwan da ba na sayarwa ba - wanda ya ɓace sakamakon zirarar ruwa, sata ko hanyar da ba a daure ta da kyau ba. Kudaden shiga da aka rasa za su iya ba da kuɗi don faɗaɗa bayar da ruwan zuwa unguwannin kamar na Mireille.
Dokar ba ta da wani tasiri: ƙasa da rabin ƙasashe suna buga rahotannin jama'a kan ingancin ruwan sha.
"Miliyoyin rayuka suna ci gaba da salwanta kowace shekara," in ji Dr Ruediger Krech na WHO.
Ambaiya da cututtuka
Sauyin yanayi yana ƙara ta'azzara kowace gazawa. Rahoton ya gano cewa kashi 80% na ƙasashe yanzu suna ambaton hatsarin yanayi a cikin manufofinsu na ruwa, tsaftar jiki da tsaftar muhalli, amma kashi 20% ne kawai ke da matakan da za su tallafa wa al'ummomin da suka fi rauni.
Gibin da ke tsakanin fahimtar matsalar da daukar matakin gyara na da fadi sosai.
A unguwar da Duncan yake, wannan ba wani abu ba ne da za a iya fahimta. Ruwan sama mai ƙarfi yana mamaye ƙasa mai ƙasƙanci, yana gurɓata hanyoyin ruwa marasa zurfi da kuma lalata kayayyakin tsafta masu rauni. Ruwan sama na da damuna na haifar da barkewar cututtuka.
Yawan rashin lafiya ya riga ya yi yawa. A shekarar 2019, aƙalla mutane miliyan 1.4 sun mutu sakamakon abubuwan da za a iya hana su da suka shafi rashin tsaftar ruwa da rashin tsaftar muhalli.
A shekarar 2024, an ruwaito cewa sama da mutane 560,000 sun kamu da cutar kwalara a duk duniya, tare da barkewar manyan cututtuka a ƙasashe da dama na Afirka.
Matakin gyara bisa tsari
Rahoton GLAAS, wanda aka fitar shekara guda kafin taron ruwa na Majalisar Dinkin Duniya na 2026 wanda aka shirya a watan Disamba, ya bayar da hujjar yin garambawul ga tsarin.
"Haɓaka ci gaba ya dogara ne da tsarin WASH da sassa masu ƙarfi, gami da kuɗaɗen shiga, manufofi, shugabanci, iya aiki da bayanai," in ji Cecilia Scharp ma’aikaciya a UNICEF.
A ra’ayin Mireille da Duncan, tsarin da ya fi ƙarfi zai zama wani abu mai sauƙi: ruwa daga famfo, bayan gida mai ƙofa.
Rahoton ya bayyana karara cewa matsalar ba ƙarancin tsare-tsare ba ce, matsala ce ta gazawar gina cibiyoyi, kasafin kuɗi da kayayyakin more rayuwa waɗanda ke mayar da tsare-tsare zuwa famfo.
"Mun gaji da jiran abubuwa su faru," in ji Mireille. "Muna buƙatar ruwa mai tsafta da ke gudana ta famfunanmu da tsarin tsafta wanda ba ya barin mu ga fuskantar barkewar cututtuka."













