Gidauniyar Gate da OpenAI sun ƙaddamar da shirin inganta lafiya ta hanyar fasahar AI a Afirka
Gidauniyar Gates da kamfanin OpenAI sun ƙaddamar wani shirin haɗin gwiwa na dala miliyan 50 don taimakawa ƙasashen Afirka amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI don ƙarfafa tsarin kiwon lafiya don rage raɗadin tallafin manyan ƙasashen duniya.
Gidauniyar Gates da kamfanin OpenAI sun ƙaddamar shirin haɗin gwiwa na dala miliyan 50 don taimakawa ƙasashen Afirka da dama hanyoyin amfani da fasahar AI don inganta tsarin kiwon lafiyarsu da kuma rage tasirin rage tallafin ƙasashen duniya, in ji Bill Gates a ranar Laraba.
Shirin haɗin gwiwar, mai suna Horizon1000, yana shirin yin aiki tare da shugabannin Afirka don tantance yadda za a yi amfani da fasahar, kana ana ran soma wa daga ƙasar Rwanda.
"A ƙasashe matalauta da ke da ƙarancin ma'aikatan lafiya da rashin kayayyakin more rayuwa na tsarin kiwon lafiya, fasahar AI na iya zama abin da zai canza yanayin faɗaɗa hanyoyin samun kulawa ta lafiya mai inganci," a cewar Gates a wani sako da aka wallafa a shafinsa kan sanarwar ƙaddamar da shirin.
A yayin zantawarsa da kamfanin dillacin labarai na Reuters a Davos a ranar Laraba, Gates ya ce AI na da damar taimakawa wajen dawo da duniya kan turba bayan da aka rage tallafin jinƙai da manyan ƙasashen duniya ke bayarwa a bara, wanda hakan ya haifar da ƙarin mace-macen yara.
Rage tallafin ƙasashen duniya ya soma ne daga Amurka a farjon 2025, sai kuma daga baya wasu ƙasashen suka biyo sahu kamar Birtaniya da Jamus.
Gabaɗaya dai tallafin ƙasashen duniya ga fannin lafiya ya ragu zuwa kashi 27 cikin 100 a bara idan aka kwatanta da 2024, in ji Gidauniyar Gates.
AI na iya zama mai matuƙar muhimmanci a ƙasashen da wannan raguwar tallafin ta shafa, in ji Gates.
Kazalika ya ƙara da cewa "ta hanyar amfani da kirkire-kirkire, da fasahar AI, ina ganin za mu iya komawa kan hanya," kamar yadda ya fada a ranar Laraba, yana mai cewa fasahar za ta kawo sauyi a fannin kiwon lafiya.