Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya gana da takwaransa na Nijeriya Tuggar
Ministocin biyu sun gana ne a Ankara babban birnin Turkiyya a ranar Litinin.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya gana da takwaransa na Nijeriya, Yusuf Maitama Tuggar, a babban birnin ƙasar Ankara ranar Litinin. Wannan ita ce ziyara ta farko da Tuggar ya kai ƙasar Turkiyya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta wallafa hotunan ganawar a kafafen sada zumunta, amma ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.
An ƙulla alaƙar diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Nijeriya a ranar 9 ga Nuwamban, 1960. Cinikin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ya kai dala miliyan 688.4 a cikin watanni 11 na farkon shekarar 2025.
Idan aka haɗa da cinikin makamashi, Nijeriya ta zama babbar abokiyar ciniki ta Turkiyya a yankin Afirka a shekarar 2025.
Fiye da kamfanonin Turkiyya 50 ne ke aiki a Nijeriya, inda jumullar jarin da suka zuba ya kai kimanin dala miliyan 400. A ‘yan shekarun nan, an samu ƙaruwa mai yawa a ayyukan da ‘yan kwangilar Turkiyya ke gudanarwa a Nijeriya, inda darajar waɗannan ayyuka ta kusan kaiwa dala biliyan 3.
Bisa goyon bayan Ankara ga ƙoƙarin Abuja na yaƙi da ta’addanci, haɗin gwiwa a fannoni na soja, tsaro da masana’antar tsaro na ci gaba da ƙarfafa cikin tsari mai ƙarfi da ɗorewa.
Daga shekarar 1992 zuwa 2023, ɗaliban Nijeriya 199 ne suka kammala karatunsu ta hanyar tallafin karatu na Turkiyya. A halin yanzu, ɗaliban Nijeriya 149 na ci gaba da karatu a Turkiyya ƙarƙashin shirin.